Kungiyar Kwadago Ta Yi Martani Kan Karin Farashin Kudin Man Fetur, Ta Gargadi Gwamnatin Tinubu

Kungiyar Kwadago Ta Yi Martani Kan Karin Farashin Kudin Man Fetur, Ta Gargadi Gwamnatin Tinubu

  • Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyana cewa sam ba za ta saɓu ba ƙarin farashin man fetur da aka yi a ƙasar nan
  • Ƙungiyar ta yi nuni da cewa farashin komawar farashin litar mai zuwa N617 ba abu bane wanda ƴan Najeriya za su kauda kai su amince da shi ba
  • Ƙungiyar ta ɓuƙaci shugaba Tinubu da ya yi gaggawar dawowa daga hanyar da ya ɗauka na ingiza farashin man fetur ɗin zuwa N1,000 kan lita ɗaya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi fatali da ƙarin kuɗin litar man fetur zuwa N617, inda ta bayyana ƙarin a matsayin abinda ƴan Najeriya ba za su amince da shi ba.

Jaridar Daily Trust tace ƙungiyar ƙwadagon a yayin da ta ke martani ta hannun shugaban sashin watsa labarai da hulɗa da jama'a, Kwamared Benson Upah, ya bayyana cewa ƙarin babbar barazana ce ga ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Abdullahi Adamu Ya Yi Magana Kan Murabus Dinsa Daga Shugabancin APC, Ya Bayyana Mataki Na Gaba

NLC ta yi magana kan karin farashin man fetur
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, Joe Ajaero Hoto: Joe Ajaero
Asali: Facebook

Ƙungiyar ta bayyana cewa ƙarin barazana ce ga kasuwanci, walwala, hanyar samun kuɗin shiga da rayuwar ƴan Najeriya wacce ta ke ta shan duka ta kowane fanni.

Ƙungiyar ƙwadagon ta shawarci gwamnatin tarayya da ta dawo daga hanyar da ta ɗauka na shilla farashin man fetur zuwa N1,000 a lita ɗaya, rahoton Leadership ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

NLC ta yi mamakin ta yadda farashin man fetur ɗin yake tafiya zai taimaki ƴan Najeriya da tattalin arziƙin ƙasar musamman yadda ake ta maganar kawo sauyin da zai amfani mutane.

NLC tace idan aka ci gaba da haka sai litar mai ta kai N1,000

Sabon farashin man fetur ɗin a cewa ƙungiyar NLC ya nuna cewa nan bada daɗewa ba zai jiyo ƙamshin N1,000 ko fiye da hakan kan lita daya. Ƙungiyar ta ƙara da cewa hakan zai ƙara tsawwala tsadar rayuwar da ake fama da ita.

Kara karanta wannan

"Ta Sauya Lambobinta": Bayan Gama Lashe Kudin Saurayin Da Ya Dauki Nauyin Karatunta, Budurwa Ta Auri Wani Daban

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin Tinubu da ta taka burki kan wannan hanyar da ta ɗauko, inda ta ƙara da cewa mutane basu jindaɗi kwata-kwata, sannan kada fa a ɗauki shirun da ta yi a matsayin gazawa ce.

An Fara Dawowa Daga Rakiyar Tinubu

A wani labarin kuma kun ji cewa ƴan Najeriya da dama sun fara dawowa daga rskiyar gwamnatin Shugaba Tinubu kan ƙarin farashin man fetur.

Mitane da dama da aka samu jin ta bakinsu sun yi Allah wadai da wannan sabon tsarin wanda zai ƙara jefa rayuwar talaka cikin ƙunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng