Layin Mai Ya Dawo a Abuja da Kano Bayan Kara Farashin Lita Zuwa N620

Layin Mai Ya Dawo a Abuja da Kano Bayan Kara Farashin Lita Zuwa N620

  • Sakamakon tsadar litar man fetur da safiyar Talata, layin shan mai ya dawo a wasu sassan Abuja da Kano
  • Da yawan motoci da sauran ababen hawa sun kaurace wa gidan man NNPC sun koma na yan kasuwa waɗanda ba su ƙara farashi ba
  • Manajan gidan man yan kasuwa da basu ƙara tsada ba a Kano ya ce suna jiran umarni ne daga hedkwata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Cunkoson layin ababen hawa ya kara dawowa a wasu sassan babban birnin tarayya Abuja sakamakon tashin farashin man fetur yau Talata.

Daily Trust ta rahoto cewa Litar man da aka riƙa sayar wa kan farashin N539 har zuwa ranar Litinin da daddare, ta koma N617 da safyar Talata a birnin Abuja.

Layi ya sake bulla a Kano da Abuja.
Layin Mai Ya Dawo a Abuja da Kano Bayan Kara Farashin Lita Zuwa N620 Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Sai dai wannan lamari ya haddasa wahala wajen neman Fetur yayin da masu motoci suka fara jera layi a gidajen man faɗin ƙasar nan musamman inda ya fi arha.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Masu Motoci Sun Kawo Cikas Yayin da NNPC Ta Ƙara Farashin Litar Man Fetur a Kano

A gidan man AA Rano da ke Anguwar Utako Abuja, motoci sun jera layi mai tsawo a ciki da wajen harabar gidan man suna jiran sayen Fetur a farashi mai rahusa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wakilin jaridar ya ziyarci gidajen mai daban-daban a tsakiyar birnin Abuja, inda ya tarad da layi a kan Tituna, lamarin da ya haddasa cunkoson ababen hawa.

Halin da ake ciki a birnin Kano

Haka zalika a birnin Kano, layi ya ɓulla a gidajen mai da dama musamman waɗanda har yanzu su ke sayar da lita a kan farashin N540, Vanguard ta rahoto.

Bayan gidan man NNPCL ya ƙara farashin lita zuwa N620, motoci da sauran ababen hawa sun koma gidan man yan kasuwa masu zaman kansu da ba su ƙara tsada ba.

Layin Man fetur ya ƙara ɓulla a Kano da Abuja.
Layin Mai Ya Dawo a Abuja da Kano Bayan Kara Farashin Lita Zuwa N620 Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Motoci sun cika gidan mai kuma layi ya kawo har waje kan tituna a gidan man yan kasuwa kamar AA Rano, Aliko Oil, Total da wasu kalilan da har yanzu su ke bada Fetur kan N540 a Kano.

Kara karanta wannan

Renewed Hope ko Wahala: An fara dawowa daga rakiyar Tinubu kan tashin kudin fetur

Menene dalilin ƙara farashin Fetur?

Manajan ɗaya daga cikin gidajen man yan kasuwa ya bayyana cewa suna jiran umarni daga sama kuma da zaran umarnin ya zo, za su bi sahu su ƙara farashin mai.

A bangaren NNPC kuma, manajan ɗaya daga cikin gidajen mai ya ce da safiyar Talata suka sami umarnin ƙara farashin kuma bayanin da aka musu shi ne yanayi ne ya sauya duba da yadda ake musanyar kuɗi.

Motoci Sun Fasa Shan Mai Yayin da Farashin Lita Ya Ƙaru a Jihar Kano

Rahoto ya nuna masu motoci da sauran ababen hawa da suka shiga ba tare sanin mai ya ƙara tsada ba sun riƙa fito wa basu siya ba a cikin jihar Kano.

Direbobi sun yi ƙorafin cewa abubuwa sun ƙara lalacewa a ƙasar nan, ba su san inda aka dosa ba a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262