Motoci Sun Fasa Shan Mai Yayin da Farashin Lita Ya Ƙaru a Jihar Kano
- Gidajen man NNPCL sun ƙara farashin litar man fetur a cikin kwaryar birnin Kano, sai dai kwastomomi sun yi watsi da ƙarin
- Rahoto ya nuna masu motoci da sauran ababen hawa da suka shiga ba tare sanin mai ya ƙara tsada ba sun riƙa fito wa basu siya ba
- Direbobi sun yi ƙorafin cewa abubuwa sun ƙara lalacewa a ƙasar nan, ba su san inda aka dosa ba a halin yanzu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano State - Da yawan motocin da suka shiga gidan man NNPC da ke Hotoro, ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano domin shan mai, sun yi kwana sun fito ba tare da biyan buƙata ba.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Motocin sun shiga gidan man da tunanin zasu sha mai a N540 kan kowace lita, bisa mamaki aka ce musu farashin lita ya ƙara tsada zuwa N620.
Da jin haka direbobin mafi akasarin motocin suka fara ja baya suna barin gidan ba tare da sun sayi man fetur ɗin ba yau Talata, 18 ga watan Yuli, 2023.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan man mallakin kamfanin mai na ƙasa NNPCL, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa, ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Yau muka wayi gari da wannan ƙarin kuma kamar yadda kuke gani kwastomomi na ficewa ba tare da sun sayi fetur din ba."
Yadda mutane suka rika guduwa daga gidan man NNPCL
Wani mai a daidaita sahu wanda aka fi sani da Keke Napep Nura Isiya ya ce, "Wannan abin dariya ne, wai ina zamu sa kanmu ne a ƙasar nan? Maganar gaskiya ba zan iya sayen mai a wannan farashin ba."
Wani direban mota mai suna, Shamsuddeen Muhammad, ya bar harabar gidan man NNPCL ba tare da ya sayi Fetur din ba.
Ya ce gara ya koma gidan man yan kasuwa masu zaman kansu waɗanda har yanzu ba su ƙara farashin lita ba.
"Haba Mallam meye haka? Na kira wani ya faɗa mun zan samu kan N540 zuwa N550 a wasu gidajen mai, yanzu zan yi hanzarin zuwa can kafin labari ya riske su, su ƙara farashi."
An gano cewa yanzu haka Tankoki 30 maƙare da man fetur sun yi fakin a wajen Defot ɗin NNPCL da ke Hotoro. Haka a gidan mai an ga motoci biyu na shirin sauke mai, Punch ta rahoto.
Bamu yi tsammanin ƙarin farashin litar mai ba
Wani mazaunin Hotoro a Kano, Malam Sanusi Isiya, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa tabbas an wayi gari da tsadar fetur da ba a taba tsammani ba bayan cire tallafi.
Malam Sanusi ya ce lokacin da ya samu labarin ƙarin da kuma yadda Motoci da yan Nafef ke fasa shan mai a gidan man NNPCL ya je da kansa don gane wa idonsa.
Ya ce:
"Eh tabbas, na je gidan man NNPCL saboda muna kusa, sun ƙara farashi har N620, dole direbobin motocin haya da 'yan Nafef suka riƙa fita suna canja gidan mai."
"AA Rano bai ƙara kuɗi ba, saboda haka idan kaje wurin layi kam iya ganin idonka. A zahirin gaskiya ba mu yi tsammanin wannan tsadar ba, bamu san ina ake son talakawa su sa kansu ba."
Shugaba Tinubu Zai Mika Sunayen Ministoci Ga Majalisar Tarayya Makon Nan
Rahoto ya ce a wannan makon shugaba Bola Ahmed Tinubu zai aika sunayen ministoci ga majalisar tarayya domin tantance wa.
Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta ce tsakanin ranakun Laraba da Alhamis ake tsammanin sunayen ministocin zasu isa majalisa.
Asali: Legit.ng