Gwamnatin Tarayya Ta Magantu Kan Karyewar Farashin Mai Bayan Dillalan Man Sun Fara Shigo Da Shi Kasar

Gwamnatin Tarayya Ta Magantu Kan Karyewar Farashin Mai Bayan Dillalan Man Sun Fara Shigo Da Shi Kasar

  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa dillalan man fetur sun fara shigo da shi kasar don samun wadatuwar shi a fadin kasar
  • Shugaban hukumar albarkatun man (NMDPRA) shi ya bayyana haka a ranar 17 ga watan Yuli inda ya ce ana sa ran farashin zai yi kasa
  • Ya ce kamfanoni 56 sun nemi lasisi don shigo da man fetur kasar bayan uku daga cikinsu sun shigo da man don saukaka wa al'umma

FCT, Abuja - Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur (NMDPRA) ta bayyana cewa dillalan man fetur a kasar sun fara shigo da man cikin Najeriya.

Hukumar ta bayyana haka ne a ranar Litinin 17 ga watan Yuli a Abuja ta bakin babban shugabanta, Faroul Ahmed, cewar Legit.ng.

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana A Kan Farashin Man Fetur Zai Yi Kasa Bayan Dillalan Mai Sun Fara Shigo Da Mai
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Kwanan Nan Farashin Man Fetur Zai Yi Kasa Saboda Kamfanoni Da Dama Sun Fara Shigo Da Shi Kasar. Hoto: Bloomberg/Contributor.
Asali: Getty Images

Gwamnatin Tarayya ta ce kamfanoni 56 ne suka nemi lasisin fara shigo da mai

Kara karanta wannan

Lauyoyi 60 Sun Yi Taron Dangi, Za Ayi Shari’a da DSS a kan Godwin Emefiele

Ya ce daga cikin kamfanoni 56 da suka nemi lasisi na shigo da man, 10 daga ciki sun himmatu a kan hakan yayin da uku suka fara shigo da mai din Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya lissafo kamfanoni ukun da suka hada da AY Ashafa da Prudent da kuma Emadeb inda ya ce kamfanoni da dama za su fara shigo da man a mako mai zuwa.

Ya ce kafin yanzu mafi yawan man da 'yan Najeriya ke amfani da shi kamfanin mai na NNPC ne ke shigo da shi, inda ya ce duk matsalolin da aka fuskanta a baya na shigo da man yanzu ya fara wucewa.

Sun roki alfarma a wurin Gwamnatin Tarayya

Vanguard ta tattaro cewa dillalan man fetur din sun roki Gwamnatin Tarayya ta kawo karshen rashin tsaro da kuma dakatar da harajin kamfanoni a kan bakin mai.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Gargruwa 2, Sun Halaka Mutane da Yawa

Sun kuma bukaci gwamnatin ta kawo karshen karancin abinci da matsalar sufuri a kasar don inganta rayuwar al'umma.

Karyewar Farashi, Rashin Ciniki Da Tarun Matsalolin Da Suka Addabi Masu Gidajen Mai Bayan Cire Tallafi

A wani labarin, tun bayan da Shugaba Tinubu ya cire tallafi, 'yan kasar suka shiga halin ni 'yasu.

Bayan wahalhalun da mutane suka sha na karancin man a kasar, daga bisani mai din ya zo ya yi tsada fiye da tunani.

Masu gidan mai suma sun koka kan yadda cire tallafin ya shafi harkokin kasuwancinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.