Sojojin Najeriya Sun Kama Babban Mota Makare Da Muggan Makamai Za A Kai Su Anambra

Sojojin Najeriya Sun Kama Babban Mota Makare Da Muggan Makamai Za A Kai Su Anambra

  • Sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wata babbar mota makare da miyagun makamai a jihar Ogun
  • An bayyana cewa an shigo da makaman ne daga kasar Mali, yayin da ake shirin kai su jihar Anambra
  • Jami’an sojin sun roki ‘yan Najeriya da su cigaba da ba su bayanai kan duk wata barazana ta tsaro da suka lura da ita

Ogun - Jami’an bataliya ta 192 ta rundunar sojojin Najeriya, ta damke makamai masu tarin yawa a yayin da ake kokarin kai su jihar Anambra, a ranar Asabar, 15 ga watan Yulin shekarar 2023.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a shafin Tuwita na rundunar tsaron Najeriya.

Sojoji Najeriya sun yi nasarar kam tarin makamai
Sojojin Najeriya sun kama makamai masu tarin yawa a jihar Ogun. Hoto: @HQNigeriaArmy
Asali: Twitter

Sojojin sun yi aiki bisa bayanai na sirri

Sojojin wadanda suka samu bayanai na sirri, sun tare titin Ajilete zuwa Owode da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa ta jihar Ogun, inda suka kama manyan bindigu da tarin albarusai a cikin wata babbar mota mai lamba ENU 697 XY.

Kara karanta wannan

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Damke Daya Daga Cikin Mutanen Da Ke Da Hannu Wajen Kashe Babban Dan Siyasa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An bayyana sunayen wadanda aka kama da Mista Eric Seworvor dan kasar Ghana, da direban motar Lukman Sani, wadanda yanzu haka suke taimakawa jami’an tsaro wajen gudanar da bincike.

A yayin da ake gudanar da bincike, an gano cewa mutanen sun dauko makaman ne daga kasar Mali, wanda suka biyo da su ta iyakar Idiroko, a kan hanyarsu ta zuwa Onitsha ta jihar Anambra, kafin dubunsu ta cika.

Sojoji sun nemi ‘yan Najeriya su ci gaba da basu bayanai kan tsaro

Ya kara da cewa jami’ansu sun yi matukar kokari wajen dakile safarar miyagun makaman da ka iya tada hankalin yankin, inda ace an yi nasarar wucewa da su.

Onyema ya yi kira ga duka ‘yan kasa na gari da su ci gaba da bai wa jami’ai bayanai a duk lokacin da suka ga wani abu da ba su gane masa ba.

Kara karanta wannan

An Damke Sarkin Arewa da Mai Dakinsa a Kudancin Najeriya Saboda Alaka da Emefiele

Shugaban sojojin Najeriya, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya jinjinawa jami’an, sannan kuma ya kara rokonsu da su kara dagewa wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Sojojin Najeriya sun halaka mayakan ISWAP da dama a jihar Borno

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton dakarun tsaron Najeriya da suka halaka mayakan ‘yan ta’addan ISWAP masu tarin yawa a wani luguden wuta da suka yi musu.

Hakan ya faru ne a yankin Marte da ke jihar Borno, inda jami’an sojojin sama suka yi ruwan wuta kan ‘yan ta’addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng