Hadiman Majalisa za su Lakume N16bn, Tinubu da Shettima za su ci Abincin N500bn

Hadiman Majalisa za su Lakume N16bn, Tinubu da Shettima za su ci Abincin N500bn

  • Yayin da ake kiran talaka ya kara hakuri, ‘Yan majalisa za su dauki Hadimai kimanin 3,0000 aiki
  • Bola Tinubu da Kashim Shettima za su kashe Biliyoyi wajen zirga-zirga da cin abinci a Aso Rock
  • Wasu su na da ra’ayin masu mulki sun cigaba da bushasha, ana kuma kawo tsare-tsare masu tsauri

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya dauki mutane fiye da matsayin masu taimakawa da bada shawara.

Daily Trust ta ce shi ma Godswill Akpabio mai jagorantar majalisar dattawa ya nada mutane da-dama da sunan Hadimai da masu ba shi shawara.

Baya ga haka akwai sauran Sanatoci 107 da ‘yan majalisar wakilan tarayya 358 da doka ta ba damar nada mutane biyar a matsayin hadimansu.

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a tashar jirgi Hoto: @ABATMediaCentre
Asali: Twitter

Tsohuwar al'ada ce a Najeriya

Ba wannan ne karon farko da shugabannin majalisa su ka tara mukarrabai ba, amma yanzu abin ya fitowa fili alhali gwamnati na kukan rashin kudi.

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an Tsaro Su Ka Cafke ‘Yan Bindiga Daga Dawowa Daga Hajji a S/Arabiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce abin da hakan yaje nufi shi ne za a samu Mukarrabai akalla 2700 a majalisar tarayya, wanda su ke karbar N700, 000 zuwa N1, 000, 000.

Hadiman su ka kula da ofisoshin ‘yan majalisar a mazabunsu kuma su na lura da koken jama’a. Wannan al’ada ta na nan har a gwamnatocin jihohi.

Aiki ko facaka da dukiya?

Kungiyoyin CISLAC, CHRICED da YPICL sun soki lamarin, su na ganin facaka ce. Akwai wasu hadiman a fadar shugaban kasa da ofishin Ministoci.

Daga cikin N328bn da ‘yan majalisa za su kashe, mukarraban da su ka nada za su samu N16.52bn, kwangilolin mazabu za su ci N100bn a shekara.

A kasafin kudin bana, Muhammadu Buhari ya ware N11.92bn domin tafiye-tafiyen shugaban kasa da na mataimakinsa da N508.7bn kan kayan abinci.

Wani rahoton ya ce dawainiyar jiragen Gulfstream GV da CL605 kadai za su ci N1.60bn a yayin da gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

Majalisa ta samu karin N70bn

A karin Naira biliyan 819 da Najeriya za ta kashe a bana, 'yan majalisa su na da 8.5%, an ce kudin za su taimaka wajen gudanar da ayyukan majalisa.

Rahoto ya zo cewa ‘Yan majalisa sun yi zama, su ka amince Gwamnatin tarayya ta batar da N70bn kan sababbin shiga domin su ji dadin fara aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng