Yan Sanda Sun Cafke Wata Da Ta Kwarawa Ma’akaciyar Su Ruwan Zafi Kan Zargin Nema Da Mijinta

Yan Sanda Sun Cafke Wata Da Ta Kwarawa Ma’akaciyar Su Ruwan Zafi Kan Zargin Nema Da Mijinta

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta yi nasarar cafke wata mata da ake zargi da kwarawa ‘yar aikinsu tafasasshen rowan zafi a jiki
  • Wacce ake zargin Esther Godwin ta kwarawa matar ne kuma mai shayarwa rowan zafi bisa zargin ta na alaka ta badala da mijinta
  • Kakakin rundunar a jihar, Funmilayo Odunlami ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta yi alkawarin tasa keyar ta zuwa kotu bayan gama bincike

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Jamian ‘yan sandan jihar Ondo sun kama wata matar aure mai suna Esther Godwin bisa zargin kwarawa mai shawarwa Samuel Endurance tafasasshen ruwan zafi kan zargin neman mijinta.

Matar da ake zargin an kamata ne a karshen mako bayan ta kira Endurance zuwa gidanta a kauyen Olofin da ke karamar hukumar Idanre a jihar.

Kara karanta wannan

An Tsinci Gawar Wata Budurwa Bayan Sun Shafe Tsawon Dare Da Masoyinta a Dakin Otel

Rundunar Yan Sanda Sun Kama Wata Mai Da Ta Kwarawa Ma’akaciyar Su Ruwan Zafi
Jami'an Yan Sanda Sun Cafke Matar Ne Bayan Ta Kwarawa Ma’akaciyar Su Ruwan Zafi Kan Zargin Badala. Hoto: Peoples Gazette.
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa, matar ta kira Endurance a waya inda ta yaudare ta da cewa ta zo ta karbi manja daga mijinta.

Yadda matar ta kawarawa Endurance ruwan zafi a jiki saboda kishi

Bayan ta iso ne sai Esther ta karbi jaririn da ke hannunta inda ta ke tuhumarta da cewa suna da alaka ta badala da mijinta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Endurance ta bayyana mata cewa babu wata alaka ta badala a tsakaninsu kawai dai ita ‘yar aikinsa ce, cewar Tribune.

Daga bisani sai Esther ta shiga daki ta dauko buta cike da tafasasshen ruwan zafi ta kwarawa Endurance a jikinta.

'Yan sanda sun tabbatar da lamarin tare da kaddamar da bincike

An garzaya da konanniyar matar zuwa asibiti a kauyen yayin da daga bisani aka tura su zuwa babban asibitin Alade Idanre inda ta ke samun kulawa.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Hallaka Wani Dan Kasuwa A Bauchi Bayan Sace Shi Ya Gagara

Yayin da ta ke bayanin yadda abin ya faru, Endurance ta ce duk da tana aiki a gonar mijin matar, amma babu wata alaka tsakaninsu da ya wuce tsakanin ubangida da mai aiki, The Nation ta tattaro.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce za a gurfanar da wacce ake zargin zuwa kotu da zarar an kamala bincike.

'Yan Sanda Sun Kama Ma'aikatan Jinya 2 Da Mai Gadi Bisa Zargin Satar Mahaifa

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Ondo sun cafke wasu da ake zargi da satar mahaifa.

Rundunar ta ce ta kama wadanda ake zargin da suke aiki a cibiyar lafiya ta Comprehensive da ke Iwo a jihar.

Daga cikin wadanda aka kaman akwai mai gadin asibibtin da kuma ma'aikatan jinya biyu a asibitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.