Jerin Jami'o'in Najeriya 10 Da Suka Fi Inganci A 2023, Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Na Ciki

Jerin Jami'o'in Najeriya 10 Da Suka Fi Inganci A 2023, Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Na Ciki

  • Mujallar Times Higher Education (THE) da ke Burtaniya da fitar da jerin jami'o'in Nahiyar Afirka da suka yi fice
  • Mujallar ta cire jerin ta shekarar 2023 inda jami'o'in Najeriya akalla fiye da 30 suka samu shiga jadawalin ta bana
  • Jami'ar Covenant da ke jihar Ogun ita ce ta farko a Najeriya sai jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Noma da ke jihar ta biyo bayanta

Mujallar The Times Higher Education (THE) ta sanar da jerin jami'o'in Nahiyar Afirka da suka yi fice.

Jadawalin jerin sunayen jami'o'in na 2023 an fitar da su ne bayan nazari da duba yadda suke kawo maslaha a matsalolin da suka addaban yankin.

Jerin Jami'o'in Najeriya 10 Da Suka Yi Fice A Shekarar 2023, Jami'ar Arewacin Najeriya Na Ciki
Mujallar Tiimes Higher Education Ta Cire Jerin Jami'o'in Najeriya 10 Da Suka Fi Fice A Shekarar 2023, Covenant Ta Zo Na Daya. Hoto: Covenant University.
Asali: Facebook

Daga cikin jerin sunayen jami'o'in akwai na Najeriya 30 da suka samu fitowa.

Jami'ar Covenant da ke jihar Ogun ita ce ta daya a Najeriya, yayin da ta kasance ta 7 a Nahiyar Afirka.

Kara karanta wannan

Za a rina: Fitacciyar jami'a ta zama ta 2 mafi nagarta a Najeriya, shugabanta ya magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta biyu ita ce Jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Harkar Noma da ke Abeokutan jihar Ogun, yayin da jami'ar Benson Idahosa da ke jihar Edo ta zama ta uku, PM News ta tattaro.

Legit.ng ta tattaro muku jerin manya-manyan jami'o'in Najeriya 10 da suka yi fice a kasar.

1. Jami'ar Covenant - Jihar Ogun, ta 7 a Afirka

Wannan jami'a ce mai zaman kanta ta Kiristoci da ta fara aiki tun a shekarar 2002 a Ota da ke jihar Ogun.

Limamin majami'ar Living Faith, David Ouedepo shi ne mamallakin jami'ar da ke jihar Ogun.

2. Jami'ar Noma ta Gwamnatin Tarayya - Jihar Ogun, ta 26 a Afirka

Jami'ar da aka fi sani da FUNAAB na daya daga cikin jami'o'i uku da Gwamnatin Tarayya ta kirkiro a 1988.

Jami'ar ta na da tsangayoyi da dama wadanda dukkanninsu sun shafi harkar noma da kiwo ne don inganta tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

Lokaci Ya Yi: Allah Ya Yi Wa Matar Shahararran Dan Kasuwa, Dahiru Mangal, Rasuwa

3. Jami'ar Benson Idahosa - Jihar Edo, ta 30 a Afirka

Ita ma wannar, jami'ar Kiristoci ce da ke Benin City cikin jihar Edo kuma jami'a mai zaman kanta.

A baya sunan jami'ar ita ce Jami'ar Christian Faith kafin a sauya mata suna zuwa Benson Idahosa (BIU).

4. Jami'ar Nnamdi Azikiwe - Jihar Anambra, ta 31 a Afirka

Jami'ar da aka fi sani da UNIZIK ta na daya daga cikin jami'o'in Gwamnatin Tarayya a jihar Anambra.

Ta na da rassa a babban birnin jihar, Awka sai kuma wani sashe na makarantar a Nnewi.

5. Jami'ar Redeemers - Jihar Osun, ta 35 a Afrika

Jami'a ce mai zaman kanta da ke Ede cikin jihar Osun.

An kirkiri jami'ar a shekarar 2005 wanda Redeemed Christian Church of God (RCCG) suka mallaka.

6. Jami'ar Ibadan - Jihar Oyo, ta 36 a Afirka

Jami'ar Ibadan (UI) ta fara ne a matsayin Kwalegi da aka kirkira a 1948.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ya ji tausayin talaka, gwamnan APC ya kara albashin ma'aikata saboda tsadar fetur

Kafin komawarta sabon bangaren da suke yanzu, a baya ta na sashen Eleyele da ke jihar, wanda masu sarautar gargajiya da sauran mutanen gari suka bayar kyauta shekaru 999 da suka wuce.

7. Jami'ar Fasaha ta Calabar - Jihar Cross River, ta 37 a Afirka

Jami'ar Fasaha wacce aka fi sani da CRUTECH, jami'a ce ta gwamnatin jiha da ke birnin Calabar.

Jami'ar ta na ba da shaidar kammala digiri a bangaren kimiyya da fasaha da harkokin noma da ilimi da sauransu.

8. Jami'ar Obafemi Awolowa - Jihar Osun, ta 39 a Afirka

Jami'ar OAU kamar yadda aka fi sani ta na cikin jami'o'in Gwamnatin Tarayya da ke Ile-Ife cikin jihar Osun.

An bude jami'ar a shekarar 1961 a yankin Yammacin kasar karkashin shugabancin Samuel Ladoke Akintola.

An sauya mata suna zuwa Obafemi Awolowa don karrama marigayi tsohon firimiyan yankin Yammacin kasar.

9. Jami'ar Umaru Musa 'Yar Adu'a - Jihar Katsina, ta 43 a Afirka

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jirgin Sojojin Sama Ya Yi Hatsari a Wata Jihar Arewa

Jami'ar da aka fi sani da UMYU, gwamnatin jihar ta kirkireta a shekara 2006 don samar da ingantaccen ilimi a yankin.

Mataimakin shugaban jami'ar (VC) shi ne Shehu Salihu Muhammad, cewar PM News.

10. Jami'ar Adeleke - Jihar Osun, ta 45 a Afirka

Mamallakin jami'ar shi ne shahararren dan kasuwa Cif Adedeji Adeleke.

Jami'a ce mai zaman kanta da ke Ede a cikin jihar Osun da aka kirkira a 2011, jami'ar ta na dauke dalibai da ba su wuce 1,000 ba.

Jerin Jami'o'in Duniya Na 2023: Sunayen Jami'o'in Najeriya Da Suka Shiga Ciki

A wani labarin mai kama da wannan, an cire jerin jami'o'in Najeriya da suka fi inganci da daraja.

Kamar yadda Cibiyar Tantace Jami'o'i ta CWUR ta wallafa a shafinta na yanar gizo, jami'o'in Najeriya huɗu ne suka samu damar shiga cikin jerin jami'o'in.

An dai wallafa bayanan jami'o'in da suka fi ingancin ne a ranar Litinin, 15 ga watan Mayun da muke ciki.

Kara karanta wannan

Kaduna: KASU Ta Karyata Jita-jitar Kokarin Mai Da Jami'ar Ta Zama Islamiyya Bayan Sabbin Nade-nade, Ta Fadi Matakan Da Ta Bi

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.