Gwamnonin Kudu da Shugabannin Igbo Zasu Gana da Tinubu Kan Muhimmin Abu 1
- Gwamnonin shiyyar Kudu maso Gabas da shugabannin Inyamurai zasu gana da shugaba Tinubu kan matsalar da ta addabe su
- Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan neman izini daga Tinubu a Aso Villa, Abuja
- Ya ce babban abinda zai kawo su wurin shugaban kasa shi ne matsalar tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankinsu
FCT Abuja - Gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas da shugabannin Inyamurai Ibo zasu gana da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan batun taɓarɓarewar tsaro a yankinsu.
Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya bayyana haka ga masu ɗauko rahoton gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da shugaban Tinubu a Aso Villa da ke Abuja.
Uzodinma ya ce shi da sauran gwamnonin jihohi 5 da shugabannin ƙungiyar Ibo, Ohanaeze Ndigbo sun zauna suka yanke zuwa wurin Tinubu kan matsalar tsaron shiyyar.
Meyasa gwamnan Imo ya gana da Tinubu shi kaɗai?
Gwamna Uzodinma ya ce ya zo fadar shugaban ƙasa ne domin neman izini da lokacin ganawar shugabannin Kudu maso Gabas da Tinubu, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Ziyara ta tana da alaka da matsalar tsaron da muke fama da ita a ƙasar nan, Kudu maso Gabas, wanda kun sani, tana fama da tabarbarewar tsaro kama daga hare-haren yan bindiga, garkuwa da mutane da sauransu."
Wane mataka aka ɗauka a baya don tabbatar da tsaro a shiyyar?
Uzodinma ya nuna nadama kan yadda wutar rashin tsaro ke ƙara ruruwa a yankin duk kuwa da makudan kuɗi da kokarin al'umma da aka zuba don kawo karshen lamarin.
Gwamnan ya ce shugabannin Kudu maso Gabas zasu ƙai koƙon bara ga shugaban ƙasa ya taimaka musu don kawo karshen matsalar tsaro da tabbatar da zaman lafiya a yankin, Vanguard ta ruwaito.
Ana tsammanin a taron jagororin Ibo zasu ci gaba da gabatar da buƙatarsu na sakin Nnamdi Kanu, jagoran yan fafutukar kafa ƙasar Biafara, wanda ke hannun FG bisa zargin cin amanar ƙasa.
Ya Kamata Yan Najeriya Su Mara Wa Tinubu Baya, Zai Zuba Aiki, Oba Na Benin
A wani labarin na daban kuma Basaraken Benin a jihar Edo, mai martaba Ewuare II ya ziyarci shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Bayan ganawarsu, Sarkin ya buƙaci yan Najeriya su goya wa Bola Tinubu baya domin zai zuba musu ayyukan alheri.
Asali: Legit.ng