Emefiele Na Fuskantar Tuhumar Mallakar Makami Ba Bisa Ka'ida Ba

Emefiele Na Fuskantar Tuhumar Mallakar Makami Ba Bisa Ka'ida Ba

  • Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) zai ƙara gurfana a gaban kotu kan zargin mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba
  • Hukumar DSS za ta gurfana da Godwin Emefiele a gaban kotu a birnin Legas sati mai zuwa domin fuskantar tuhumar da ake masa
  • Emefiele dai ya kasance a tsare a hannun hukumar DSS tun lokacin da ta cafke shi bayan Shugaba Tinubu ya dakatar da shi

FCT, Abuja - Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, zai fuskanci tuhumar mallakar bindiga da harsashi ba bisa ƙa'ida ba, rahoton The Nation ya tabbatar.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa za a gurfanar da Emefiele a gaban kotu a birnin Legas a sati mai zuwa kan zargin mallakar makamin ba bisa ƙa'ida ba.

DSS za ta sake gurfanar da Emefiele gaban kotu
Ana zargin Emefiele da mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) a ranar Alhamis tace ta kai Emefiele kotu, amma ba ta yi bayani ba kan tuhumar da ta ke yi masa ba.

Kara karanta wannan

Emefiele: Kotu Za Ta Hukunta Tsohon Shugaban Kasa Buhari? Bayanai Sun Bayyana a Bidiyo

Sai dai, wata babbar kotun tarayya mai zamanta a Apo, birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a ta yi hukunci cewa cafke Emefiele da tsare shi da ake yi ya saɓawa doka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan na zuwa ne dai bayan wata babbar kotu mai zama a Maitama a birnin tarayya Abuja, ta umarci DSS ta kai Emefiele kotu ko ta sake shi cikin sati ɗaya.

Sabbin tuhume-tuhumen da Emefiele zai fuskanta a gaban kotu

Emefiele, a cewar majiyoyi zai fuskanci tuhuma biyu kan mallakar bindiga ƙirar (JOJEFF MAGNUM 8371) ba tare da lasisi ba, wanda hakan ya saɓawa sashi na 4 na dokar mallakar makami na shekarar 2004 wanda ya cancanci hukunci a sashi na 27 (1) (b) (i) na dokar.

Ana kuma zargin dakataccen gwamnan babban bankin da mallakar alburusai 123 ba tare da lasisi ba.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Umarci Jami'an DSS Su Yi Gaggawar Sakin Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Emefiele ya aikata laifukan ne dai a adireshin No.3B Iru Close, Ikoyi, Legas, a ranar 15 ga watan Yunin 2023.

An cafke Emefiele ne dai a ranar 10 ga watan Yuni, kwana ɗaya bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa.

Kotu Ta Umarci DSS Ta Saki Emefiele

A wani labarin kuma, wata babbar kotun tarayya a birnin tarayya Abuja ta umarci hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) da ta saki Godwin Emefiele da gaggawa.

Kotun ta yi hukunci cewa tsare Emefiele da ƴan sandan farin kayan ke yi ya haramta inda tace a sake shi da gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng