Dan Alkalin Alkalan Najeriya Ya Bi Sahun Mahaifinsa, Ya Zama Alkalin Kotu
- Ɗan babban Alkalin Alkalan Najeriya ya bi sahun mahaifinsa, ya zama Alƙalin babbar Kotun tarayya
- A taron NJC karo na 103 ranar Jumu'a, ɗan shugaban alkalai na kasa na cikin waɗanda aka zaɓa a matsayin sabbin alkalai
- Haka nan NJC ta aminta da naɗa sabbin alƙalan Kotun shari'a da ke jihohin Kaduna da Kano
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Hukumar shari'a ta ƙasa (NJC) ta naɗa ɗan shugaban alkalan Najeriya, Mai shari'a Olukayoode Ariwoola, a matsayin alkalin babbar Kotun tarayya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na ƙunshe a wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran NJC, Soji Oye, ya fitar ranar Jumu'a, 14 ga watan Yuli, 2023.
Ya ce an nɗa sabon alƙalin tare da shugaban alkalan Kotun musulunci ɗaya, alkalan babbar kotun tarayya 23 da kuma alƙalan Kotun ɗaukaka ƙara ta shari'a da ke Kano guda huɗu.
Daraktan ya yi bayanin cewa an sanar da sabbin alkalan da aka naɗa ne a ƙarshen taron NJC karo na 103 karkashin jagorancin alkalin alkalai na ƙasa, mai shari'a Ariwoola ranar Jumu'a a Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jerin mutanen da aka bada shawarin naɗa wa a matsayin alƙalai
Daga cikin mmutanen da kwamitin gwaji ya bada shawarin a naɗa alkalan babbar kotun tarayya sun ƙunshi, Ariwoola Olukayode Jnr, Ekerete Udofot Akpan, Hussaini Dadan-Garba, da Egbe Raphael Joshua.
Sauran sun haɗa da Anyalewa Onoja-Alapa, Aishatu Auya Ibrahim, Ogazi Friday Nkemakolam da kuma Ogundare Kehinde Olayiwola.
Kwamitin ya haɗa da, Chigozie Sergius, Hauwa Joeph Yilwa, Amina Aliyu Mohammed, Sharon Tanko Ishaya, Chituru Joy Wigwe-Oreh, Musa Kakaki, Owoeye Alexander Oluseyi, da Abiodun Jordan Adeyemi.
Agbaje Olufunmilola Adetutu, Salim Olasupo Ibrahim, Dipeolu Ibrahim, Dipeolu Deinde Isaac, Abdullahi Muhammad Dan-Ige da kuma Mashkur Salisu duk suna cikin waɗanda kwamitin NJC ke ganin sun cancanta.
Alkalan Kotun musulunci
A ɗaya bangaren kuma NJC ta aminta da naɗin Kadi Muhammad Aminu Danjuma a matsayin shugaban alƙalan kotun shari'a na Kaduna, kamar yadda Dailypost ta rahoto.
Sai kuma Muhammad Adam Kadem, Salisu Muhammad Isa, Isa Idris Sa’id da kuma Aliyu Muhammad Kani a matsayin alkalan Kotun daukaka ƙarar shari'a ta jihar Kano.
Daga ƙarshe Oye ya yi bayanin cewa za a rantsar da baki ɗaya sabbin alƙalan bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohin da zasu yi aiki sun sa hannu.
Kotu Ta Kori Ƙarar da Hukumar EFCC Ta Shigar da Rochas Okorocha
A wani labarin kuma Babbar Kotun Abuja ta kori ƙarar da aka shigar da tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha.
Alkalin Kotun ya ce ƙarar cin mutuncin shari'a ne saboda EFCC ta shigar da irinta gaban babbar Kotun tarayya kuma ta yanke hukunci.
Asali: Legit.ng