Zainab Da Wasu Yan Najeriya 3 Da Suka Yi Aiki Da Buhari Kuma Suka Samu Sabbin Mukamai
FCT, Abuja - Tun bayan karewar wa'adin mulkin ubangidansu a ranar 29 ga watan Mayun 2023, wasu fitattun yan Najeriya da suka yi aiki tare da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sun samu sabbin mukamai.
Yayin da mutum kamar Zaccheus Adelabu Adedeji wanda ya yi aiki karkashin gwamnatin Buhari ya samu gurbi a wajen Shugaban Kasa Tinubu domin tattara kudaden shigar Najeriya, da dama basu samu wannan damar ba.
Yan Najeriya da suka yi aiki tare da Buhari kuma suka samu sabbin mukamai
A wannan zauren, Legit.ng ta yi rubutu kan yan Najeriya da suka yi aiki tare da Buhari kuma suka samu sabbin mukamai.
Yemi Osinbajo
Legit.ng ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya samu sabon mukami makonni shida bayan ya bar fadar shugaban kasa, Abuja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Farfesa Osinbajo ya sanar da cewa an nada shi a matsayin mai bada shawara na duniya ga kamfanin Global Energy Alliance for People and Planet.
Ya sanar da hakan a ranar Talata, 11 ga watan July, ta shafinsa na Twitter @ProfOsinbajo.
Lai Mohammed
Lai Mohammed wanda ya rike Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya samu aiki da wani kamfanin ketare mai suna Ballard Partners.
A wata sanarwa da Ballard Partners ya fitar a shafinsa na Twitter, an tabbatar da cewa Alhaji Lai Mohammed ya zama daya daga cikin abokan huldarsu.
Femi Adesina
Tsohon kakakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya samu aiki kwanaki kadan bayan sauka daga mulki.
Adesina ya bayyana cewa zai fara aiki a matsayin mataimakin shugaban kamfanin jaridar Sun daga ranar 1 ga watan Satumba, 2023.
Zainab Ahmed
Tsohuwar Ministar kud karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zainab Shamsuna Ahmed ta samu aiki da bankin Duniya a matsayin babbar Darekta mai iko.
Vanguard ta kawo rahoto a farkon makon nan cewa Zainab Shamsuna Ahmed za ta zama Darekta, kwanaki bayan ta bar kujerar Minista.
Emefiele: Lauya ya bukaci DSS ta kama tsohon shugaban kasa Buhari
A wani labari na daban, mun ji cewa an bukaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kama tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lamarin dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Barista Kingdom Okere ne ya yi wannan kiran yayin wata hira a shirin kalaci na Arise TV a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng