“8k Almajirantar Da Kasar Za Ta Yi”: Shehu Sani Ya Fadi Abin Da Mutane Za Su Yi Kafin Karbar Tallafin Tinubu
- Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya fadawa ‘yan Najeriya abin da ya kamata su yi kafin su karbi kudin rage radadin cire tallafi na Tinubu
- A ranar Alhamis 14 ga watan Yuli, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da ware N500bn don rabawa ‘yan kasar da niyyar rage musu radadin cire tallafin mai
- Shehu Sani ya ce idan za a iya tunawa a lokaci tsohon shugaban kasa, Buhari wadanda suka karbi N10,000 sun kare a cikin matsanancin talauci
Jihar Kaduna – Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani ya bayyana shirin bayar da tallafin rage radadi na Shugaba Bola Tinubu a matsayin almajirantar da kasar.
Shugaba Tinubu a ranar Alhamis 14 ga watan Yuli ya sanar da ba da tallafin N8,000 har na tsawon watanni shida ga gidaje miliyan 12, cewar Legit.ng.
Sani ya bayyana haka a shafinsa na Twitter inda ya bukaci ‘yan Najeriya su yi addu’a kafin karbar kudin.
Ya ce lokacin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari wadanda suka karbi N10,000 da ya ke rabawa daga baya sun kare a cikin matsanancin talauci fiye da wadanda ba su karba ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da ce wannan N8,000 da ake magana ba komai ba ne illa almajirantar da kasar Najeriya da shugaban ke son yi.
Ya ce:
“Mutanen da suka karbi N10,000 na Buhari sun kare cikin matsanancin talauci, ku yi addu’a kafin ku karbi N8,000 din nan.”
Ya kara da cewa:
“Naira Dubu takwas almajirantar da kasar ce.”
Idan ba a manta ba Shugaba Tinubu ya yi alkawarin samar da wani tallafi da zai rage radadin wahalar da mutane suka sha bayan an cire tallafin mai a kasar.
Masu fashin baki a kasar sun soki wannan tsari inda suka ce wannan shiri asara ne kawai babu wani abin da zai rage saboda kankantar kudin.
Wasu sun ba da shawarar a yi amfani da kudin wurin inganta wasu masana’antu don samar da ayyukan yi ga matasa.
Cire Tallafi: ’Yan Najeriya Sun Kushe Shirin Tinubu Na Raba N8000 Ga Gidaje 12m
A wani labarin, yayin da Shugaba Bola Tinubu ya ware N500bn don rage radadi, 'yan kasar sun kushe tsarin.
Shugaba Tinubu ya ware kudaden ne don rabawa gidaje miliyan 12 kudi N8,000 har na tsawon watanni shida.
Masu fashin baki sun bayyana tsarin a matsayin shirme wanda zai zama asara ganin yadda kudaden babu abin da za su rage.
Asali: Legit.ng