Kaduna: KASU Ta Musanta Zargin Musuluntar Da Jami'ar Bayan Sabbin Nade-nade, Ta Bayyana Tsarin Da Ta Bi
- Hukumar jami'ar jihar Kaduna ta musanta zargin jita-jitar da ake yadawa na son kai a nade-naden mukamai
- Ana zargin hukumomin makarantar da Musuluntar da jami'ar ganin yadda ta yi nade-naden mukamai ba ka'ida
- Magatakardar jami'ar, Samira Balarabe ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Juma'a 14 ga watan Yuli
Jihar Kaduna - Hukumomin Jami'ar Jihar Kaduna (KASU) sun roki al'umma da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa na Musuluntar da jami'ar.
Magatakardar jami'ar, Samira Balarabe ita ta bayyana haka a yau Juma'a 14 ga watan Yuli a Kaduna.
Ta ce dukkan mukaman da aka raba na shugabannin jami'ar an bi ka'ida da kuma cancanta, cewar Daily Nigerian.
Hukumar KASU ta yi fatali da zargin
Ta kara da cewa, gwamnan jihar ya amince ne da nadin mukaman bayan an bi ka'ida da kuma tantancewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce nada shugaban jami'ar da mataimakinsa ya samu amincewar majalisar zartaswa na jami'ar ne kafin ba da mukamnan.
Ta ce:
"Majalisar zartaswa ce ta amince da nadin mataimakin shugaban jami'ar."
Samira ta ce nadin ya biyo bayan zaben da aka gudanar na adalci a ranar 6 ga watan Yuli.
Ta bayyana yadda jami'ar ke gudanar da ayyukanta
Sanarwar ta kara da cewa:
"Hukumar makarantar ta himmatu wurin inganta jami'ar ta fannin koyarwa da bincike da kuma samar da kudaden shiga.
"Jami'ar na kan gaba wurin kawo sabbin tsare-tsare na bincike don inganta basirar dalibai da tunaninsu."
Ta ce a kwanan nan KASU ta samu nasarori da dama da suka mayar da ita sahun gaba a jerin jami'o'in da suke wannan yanki, Daily Trust ta tattaro.
MURIC Ta Zargi Gwamna Adeleke Na Jihar Osun Da Yi Wa Kungiyar CAN Aiki
Za a rina: Gwamna ya umarci farfesan halayyar dan Adam ya zauna da dalibar da ta kara sakamakon JAMB
A wani labarin, Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta zargi gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da son kai a mukamai.
Kungiyar na zargin gwamnan da nuna fifiko na mukaman kwamishinoni da ya fitar a jihar.
Ta ce a cikin jerin sunayen kwamishinonin akwai Kiristoci 17 yayin da Musulmai ba su wuce bakwai ba.
Asali: Legit.ng