Tashin Kuɗin Wutar Lantarki Zai Tabbata, Kamfanoni Sun Buƙaci a Canza Farashi

Tashin Kuɗin Wutar Lantarki Zai Tabbata, Kamfanoni Sun Buƙaci a Canza Farashi

  • Alamu sun tabbatar da cewa da kamar wuya a ce farashin da ake sayen wutar lantarki bai tashi ba
  • Kamfanonin DisCos da ke da alhakin raba wuta sun nemi gwamnati ta bada damar sake duba farashi
  • A karshe sai dai farashin shan wutan ya tashi a sakamakon tsadar kaya a kasuwa da tashin Dalar Amurka

Abuja - A ranar Alhamis da ta gabata, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa kamfanonin raba lantarki sun bukaci a duba farashin shan wuta.

Kamfanonin da aka fi sani da DisCos su na so gwamnatin Najeriya ta amince masu sauya farashi a sakamakon canjin da aka samu a kasuwancinsu.

Kamar yadda Punch ta fitar da rahoto a yau, sababbin tsare-tsaren tattalin arziki da aka fito da shi su na da tasiri kan yadda ake sayen wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Radadin Cire Tallafi: Martanin 'Yan Najeriya Kan Aniyar Tinubu Na Raba N8000 Ga Gidaje 12m

Wutar lantarki
Tashar wutar lantarki Hoto: Getty/FLORIAN PLAUCHEUR
Asali: AFP

DisCos sun aikawa NERC takarda

Hukumar NERC ta bayyana cewa kamfanonin DisCos sun bada dalilinsu na neman a ba su dama su canza farashin yadda suke saidawa jama’a wuta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan yana zuwa ne bayan da farko wasu daga cikin kamfanonin sun yi gaggawar sanar da shirin canza farashi, kafin su lashe aman na su daga baya.

A dokar lantarki, sai NERC tayi na’am sannan kamfanoni za su iya canza farashin wuta.

Rahoton da mu ka samu daga Business Day ya ce kamfanonin raba wuta 11 su ka rubutawa gwamnati takarda domin su samu damar canza farashi.

Meya jawo tashin farashin?

DisCos na kukan an samu bambancin 22.41% a kudin kasar waje, Dala ta koma N785/$1 maimakon N400/$1 da suka saba saye kafin watan Mayu.

Kamfanonin sun dogara da sashe na 116 (1) da kuma 2(a&b) na dokar lantarki ta 2023 wajen kara kudi domin ganin sun samu ribar kasuwancinsu.

Kara karanta wannan

Hadimar Tinubu Ta Ayyana Bangaren da Gwamnatin APC Za Ta Maida Hankali a Kai

Tashar talabijin Channels ta ce NERC mai sa ido a madadin gwamnati za ta saurari bukatar kamfanonin, ta na kuma maraba da shawarar jama’a.

Kamar dai yadda doka ta bada dama, al’umma na da damar zuwa su tofa albarkacin bakinsu a lokacin yanke sabon farashin saida wuta a kasar.

Shari'ar Zaura da EFCC

‘Dan takaran Sanatan Kano ta tsakiya a APC a 2023, Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya dauki Lauya kuma ya yi nasarar dakatar da sauraron kararsa.

Bayan ya rasa shari’ar kujerar majalisa, labari ya zo cewa EFCC ta sake maida A. A Zaura kotu, amma dole a jira kotun koli kafin cigaba da shari’arsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng