"Toyota Corolla & Wasu Motocci 11 Da Basu Shan Mai Sosai": Dan Najeriya Ya Lissafa Motocci Masu Saukin Sha'ani
- Wani ɗan Najeriya ya janyo muhawara mai daɗi a Tuwita yayin da ya lissafo motoci 12 masu sauƙin shan mai
- Daga cikin motocin da ya lissafo akwai Kia Rio, Peugeot 208, Hyundai Sonata, Honda City, da Toyota Corolla
- Wasu 'yan Najeriyan sun ƙara bayyana ƙarin wasu motocin marasa shan mai sosai baya ga waɗannan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani ɗan Najeriya ya janyo muhawara mai daɗi a dandalin Tuwita, sakamakon batun motoci Masu sauƙin shan man fetur da ya ɗauko.
'Yan Najeriya da dama na ta fafutukar ganin sun samu hanyar da za su rage amfani da mai sosai saboda cire tallafi da aka yi.
A kwanakin baya 'yan Najeriya da dama sun nuna jin daɗinsu dangane da tsarin nan da ke bai wa mutum damar juya injin motarsa ya koma mai amfani da iskar gas daga na Fetur.
Jerin fitattun motoci 12 masu sauƙin shan man fetur
Rubutun da matashin mai suna oku yungx ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya sanya 'yan Najeriya da dama bayyana ra'ayoyinsu kan kalar motar da suka fi sha'awa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Waɗannan su ne motoci 12 masu sauƙin shan mai kamar yadda ya lissafa su:
1. Honda Civic
2. Toyota Corolla.
3. Toyota Yaris.
4. Kia Rio
5. Volkswagen Golf.
6. Toyota Prius.
7. Hyundai Elantra.
8. Peugeot 208.
9. Honda City.
10. Hyundai Sonata.
11. Mazda 3.
12. Kia Optima.
Masu amfani da Tuwita sun to fa albarkacin bakinsu game da motoci masu sauƙin shan fetur
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin mutane mabanbanta dangane da wannan batu na motocin da aka ce suna dau sauƙin shan man fetur.
Dalla-Dalla: Yadda Dokar Ta Ɓacin da Tinubu Ya Ayyana Kan Samar da Abinci Zata Taimaka Wa Yan Najeriya
@teejayviruz ya ce:
"Zan iya shaida hakan a kan Honda civic."
@IAmVirgoBoi ya ce:
"Akwai Toyota Camry da kuma Toyota Sienna ma."
@luqmAnpetersFSG ya ce:
"Ka ga Toyota Yaris kuwa? Da ita na riƙa zuwa Unilorin daga Legas zuwa da dawowa in na cika tanki, tun daga lokacin nake mutunta motar kuma na ƙara sonta.”
@RonOkorie ya ce:
"Yawancin motocin da ke nan masu ɗaukar lita 1.8 ko ƙasa da haka, ba za ka sayi mota mai injin da ke ɗaukar lita 2.5 ba kuma ka yi tsammanin zaka samu sauƙin shan mai."
@lovedoctor_dee ya yi tambaya:
"Zan iya samun ɗaya daga cikinsu akan ƙasa da miliyan biyu?"
@preach_peace_ ya ce:
"Kamata ya yi a fara kawo Toyota Yaris da Hyundai Elantra kafin kowace mota."
Makaho mai gyaran mota ya bayyana yadda yake gane matsalar mota
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan wani makaho mai basira da ya shafe shekaru da dama yana gyaran mota a Abuja babban birnin tarayya.
Makahon a wani ɗan gajeren bidiyo, ya bayyana cewa yana iya gane matsalar mota daga sauraron kukan da injinta yake yi.
Asali: Legit.ng