Majalisar Dattawa Ta Amince Da Nadin Hafsoshin Tsaron Kasa

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Nadin Hafsoshin Tsaron Kasa

  • Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin da Shugaba Tinubu ya yi wa hafsoshin tsaro bayan ya kori magabatansu
  • Babban hafsan tsaro na ƙasa, Manjo Janar Christopher Musa, da sauran hafsoshin tsaron da aka naɗa sun bayyana a gaban majalisar a Abuja
  • Manjo Janar Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron sun keɓe da ƴan majalisun domin tantance su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Majalisar dattawa a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli ta amince da naɗin Manjo Janar Christopher Musa a matsayin babban hafsan tsaro na ƙasa (CDS) bayan zaman tantancewa har na sa'o'i uku.

Majalisar dattawan a ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio ta kuma tabbatar da amince da naɗin hafsoshin tsaro wanda Shugaba Tinubu ya naɗa, cewar rahoton The Nation.

Majalisar dattawa ta amince da nadin sabbin hafsoshin tsaro
Sabbin hafsoshin tsaro lokacin da su ke shiga majalisa Hoto: Thenation.com
Asali: UGC

Makalisar dattawa ta amince da naɗin Manjo Janar Lagbaja da sauran hafsoshin tsaro

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Manyan Hafsoshin Tsaron Da Shugaba Tinubu Ya Nada

Hafsoshin tsaron da majalisar dattawan ta amince da naɗin su sun haɗa da Manjo Janar Taoreed Lagbaja a matsayin shugaban hukumar sojin ƙasa ta Najeriya (COAS), Rear Admiral E. A Ogalla, a matsayin shugaban hukumar sojojin ruwa ta ƙasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran su ne AVM H.B Abubakar, a matsayin shugaban hukumar sojin saman Najeriya, DIG Kayode Egbetokun, muƙaddashin sufeta janar na rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP) da Manjo Janar EPA Undiandeye, shugaban hukumar tattara bayanan fasaha ta ƙasa. rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Shugaba Tinubu a ranar Talata, 11 ga watan Yuli ya buƙaci majalisar dattawan da ta tantance hafsoshin tsaron domin tabbatar da naɗin da ya yi musu

Ƙafin a amince da naɗin na su, hafsoshin tsaron sun yi keɓe da ƴan majalisun tun daga misalin ƙarfe 12:42 na rana zuwa ƙarfe 3:00 na rana.

Kara karanta wannan

Miji Da Mata Sun Yi Basajar Shiga Musulunci Yayin Da Suka Tafkawa Liman Sata a Yobe

A cikin wannan lokacin ne ƴan majalisun suka tabbatar da naɗin da shugaba Tinubu ya yi wa hafsoshin tsaron.

Majalisa Ta Fara Tantance Hafsoshin Tsaro

Tun da farko rahoto ya zo cewa majalisar dattawa ta fara tantance sabbin hafsoshin tsaron ƙasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa.

Tantancewar ta su na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya aike da wasiƙa zuwa ga majalisar domin ta amince da naɗin da ya yi musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng