Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Ekiti Da Aka Sace Ya Shaki Iskar 'Yanci

Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Ekiti Da Aka Sace Ya Shaki Iskar 'Yanci

  • Shugaban jam'iyyar APC na jihar Ekiti da ƴan bindiga suka sace ya shaƙi iskar ƴanci bayan kusa kwana huɗu a tsare
  • Mr Paul Omotoso ya kuɓuta ne tare da sauran mutum biyun da ƴan bindigan suka yi awon gaba da su a tare
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da cafke wasu mutum uku da ake zargi da sace shugaban jam'iyyar da sauran mutanen

Jihar Ekiti - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Ekiti, Mr Paul Omotoso da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su sun shaƙi iskar ƴanci, rahoton Leadership ya tabbatar.

Shugaban jam'iyyar ta APC da sauran mutanen sun kuɓuta ne bayan an sace su a ranar Asabar da ta gabata inda suka shafe kusan kwanaki huɗu a hannun ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Miji Da Mata Sun Yi Basajar Shiga Musulunci Yayin Da Suka Tafkawa Liman Sata a Yobe

Shugaban APC ya kubuta daga hannun 'yan bindiga
Mr Omotoso ya kubuta bayan kusan kwanaki hudu a hannun 'yan bindiga Hoto: Leadership.com
Asali: UGC

A ranar Asabar ne dai ƴan bindiga suka yi awon gaba da shugaban jam'iyyar tare da wasu mutum biyu lokacin da yake tafiya akan titin hanyar Agabado-Imesi a jihar Ekiti.

Tawagar jami'an tsaro da ta haɗa da ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro ce ta ceto mutanen daga hannun ƴan bindiga, cewar rahoton New Telegraph.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwana biyu bayan an sace su, ƴan bindigan sun tuntuɓi iyalan Omotoso da sauran mutum biyun, inda suka buƙaci da a biya su kuɗin fansa har N20m kafin su sake su.

Rundunar ƴan sandan jihar Ekiti ta tabbatar da ceto mutanen

Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da sako mutanen inda tace tuni har an sada su da iyalansu.

Rundunar ta bayyana cewa an cafke wasu mutum uku da ake zargin suna da hannu a cikin sace mutanen da aka yi.

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Bindiga Masu Yawa a Jihar Arewa, Sun Kwato Muggan Makamai

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ekiti, DSP Sunday Abutu, ya fitar, ya tabbatar da cewa an cafke mutum uku da ake zargin suna da hannu a lamarin.

Ya bayyana cewa waɗanda ake zargin na bayar da muhimman bayanai da za su sanya a cafko ainihin waɗanda ake zargi da kitsa lamarin bayan sun arce.

Sai dai, kakakin rundunar ƴan sandan bai yi bayanin cewa an biya kuɗin fansa ba ko ba a biya ba kafin a sako shugaban jam'iyyar da sauran mutanen.

Sojoji Sun Halaka 'Yan Bindiga a Jihar Plateau

A wani labarin na daban kuma, dakarun sojoji sun murƙushe wasu miyagun ƴan bindiga a wata arangama a jihar Plateau.

Dakarun sojojin sun sheƙe ƴan bindigan ne mutum uku tare da ƙwato muggan makamai a wata musanyar wuta da suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng