NLC Za Ta Sa Ƙafar Wando Ɗaya da Bola Tinubu, An Buƙaci Karin 300% a Albashi

NLC Za Ta Sa Ƙafar Wando Ɗaya da Bola Tinubu, An Buƙaci Karin 300% a Albashi

  • ‘Yan NLC da TUC ba su gamsu da matakin da aka dauka wajen rage radadin cire tallafin man fetur ba
  • Kungiyoyin da wasu ‘yan kasuwa su na ganin Naira Biliyan 500 da ake neman kashewa ba za su isa ba
  • Ma’aikata su na so ayi masu karin akalla 300% a albashi, gwamnati ba ta tsaida matsaya ba tukuna

Abuja - Kungiyoyin ‘yan kwadago watau NLC da TUC ta ‘yan kasuwa sun nuna ba su yarda a kashe N500bn domin rage radadin cire tallafin man fetur ba.

Wadannan kungiyoyi na ganin kudin da gwamnatin tarayya ta ware ya yi kadan idan aka duba wahalar da jama'a ke sha, Punch ta fitar da labarin nan.

Abin da ma’aikatan kasar su ke so shi ne ayi kowa karin 300% a cikin albashinsu domin a iya girgije tsadar rayuwan da aka shiga a dalilin tashin fetur.

Kara karanta wannan

Sakataren APC Ya Jero Irin Mutanen da Shugaban Kasa Zai Dauko Su Zama Ministoci

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya cire tallafin fetur Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Abin da 'Yan NLC su ke so

Kwamred Hakeem Ambali ya zanta da Punch, ya ce rabin Tiriliyan ba za ta isa mutum miliyan 125 wanda su ke rayuwa cikin kungurmin talauci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambali shi ne Ma'ajin NLC na kasa, ya ce ana bukatar karin albashi da kuma bashin jari ga kananan 'yan kasuwa, sannan a taimakawa manoma a kasar.

Wata shawara da ya kawo ita ce a karkata daga fetur kuma a gyara matutun mai.

Kungiyar NACCIMA ta tanka

Olusola Obadimu wanda shi ne Darekta Janar na kungiyar NACCIMA, ya yaba da Bola Tinubu kan yunkurinsa na kashe N500bn domin a iya rage radadin.

Sai dai jaridar ta ce Obadimu yana mamakin yadda za a bi wajen kashe wadannan kudi, ya ce sai ya ga tsarin da aka yi sannan zai iya cewa wani abu tukun.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata: Majalisa Za Tayi Binciken Yadda Aka Saida Kadarorin Gwamnati

Ganin yadda aka karya Naira kuma aka tashi farashin man fetur, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na Legas, Gabriel Idahosa yana ganin kudin sun yi kadan.

Bola Tinubu ya nuna cewa ya san al’umma su na cikin wani mawuyacin hali, amma ya yi alkawari nan gaba kowa zai ji dadin wannan mataki da ya dauka.

Kwastam ta bude iyakoki?

Rahoto ya zo cewa shugaban kwastam, Adewale Bashir Adeniyi ya ce za ayi bincike domin a duba tasirin rufe iyakokin kasa da aka yi a gwamnatin baya.

Adewale Bashir Adeniyi ya ce har yanzu wasu kadan daga cikin iyakokin kasar nan ne a bude, akasin abin da mutane su ke tunani na wangale iyakokin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng