"Na Ga Peter Obi A Ankwa": Sanannen Fasto Ya Yi Bushara, Ya Ba Shi Shawarar Matakin Da Zai Dauka
- Wani limamin majami'a a jihar Lagos ya ce tabbas ya yi mafarki inda ya ga dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi da ankwa
- Ya ce ya gani da idonsa an saka ankwa a hannun Peter Obi kuma a tsare a ofishin Hukumar Farin Kaya ta DSS a Abuja
- Ya shawarci Peter Obi da ya yi hankali da irin maganganunsa da kuma hirar da ya ke da 'yan jaridu, don za su yi amfani da maganarsa a kansa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Lagos - Wani Fasto a jihar Lagos, Elijah Bamidele Ilukholor ya ce ya yi mafarki ya ga dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi a cikin ankwa.
Yayin wa'azi a majami'arsa da ke Lagos, Bamidele ya shawarci Peter Obi ya bi a hankali akwai alamun zai fada hannun jami'a Farin Kaya ta DSS a Abuja.
Ya ce ya ga Peter Obi a cikin ankwa kuma zai iya yiyuwa DSS su kama shi, inda ya a yi fatan kada matsalarsa ta fi ta Nnamdi Kanu, cewar Legit.ng.
Faston ya bayyana yadda ya ga Peter Obi a ankwa
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na ga Peter Obi da ankwa a hannunsa.
"Wannan shi ne shawara ta, ka yi a hankali, zan iya cewa taron dangi? Don na gan shi a hannun DSS, saboda kada matsalarsa ta fi ta Nnamdi Kanu, na gani da ido na.
"Peter Obi ya kamata ya kula da maganganun sa da hirar da ya ke da 'yan jaridu, za su yi amfani da maganarsa a kansa."
Ya ba wa Peter Obi shawarar matakin da zai dauka
Ya ce tabbas akwai wani abin da ke gudana a kasa, dole ya kula sosai da irin maganganunsa da hirarraki da yake yi, kamar yadda aka wallafa a kafar Facebook.
Faston ya kara da cewa:
"Na ga ankwa a hannunsa, kuma a tsare a ofishin DSS.
"Peter Obi ka yi hankali da irin hirar da ka ke da 'yan jaridu."
Har Yanzu Peter Obi Yafi Tinubu, Atiku Da Saura Cancanta
A wani labarin, an bayyana dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi a matsayin wanda ya fi cancanta.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo shi ya bayyana haka inda ya ce Obi ya fi Tinubu da Atiku da sauran 'yan takara kyau.
Obasanjo ya ce ya so ace Peter Obi ne ya yi nasara saboda yadda kasar za ta hau kan hanya madaidaiciya.
Asali: Legit.ng