Jami’an Gwamnati Sun Dura Gareji, An Yi Awon Gaba da Motocin Tsohon Gwamna

Jami’an Gwamnati Sun Dura Gareji, An Yi Awon Gaba da Motocin Tsohon Gwamna

  • Kwamitin karbo kadarorin da aka kafa a jihar Benuwai ya yi gaba da motocin Samuel Ortom
  • Wannan ya na cikin binciken da Gwamantin Hyacinth Alia take yi, hakan ya jawo PDP tayi martani
  • Gwamnatin Alia ta na ikirarin karbo dukiyoyin al’umma, jam’iyyar adawa ta kira abin da zalunci

Benue - Kwamitin karbo kadarori da Gwamna Hyacinth Alia ya kafa a jihar Benuwai ya kutsa wani garejin motoci da Samuel Ortom ya mallaka.

Rahoton Daily Trust ya ce ana zargin tsohon Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom ya mallaki wannan shagon motoci da yake birnin Makurdi a jihar.

‘Yan kwamitin sun dauke wasu motoci da su ka shiyarci shagon, ana zargin an yi amfani da jan-wai ne wajen dauke su saboda an gagara tuka su.

Motoci
Wasu motoci a kasar waje Hoto: www.livingmagazine.net
Asali: UGC

Raddin da PDP ta yi

Kara karanta wannan

Kujerar Shugaban APC Na Tangal-Tangal Bayan Wata 15, Zai San Makomarsa a NEC

Nan take aka ji jam’iyyar hamayya ta PDP ta maida martani, ta na zargin Gwamnatin Rabaren Hyacinth Alia da yi wa magabacinsa bita da kulli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren yada labaran PDP na reshen Benuwai, Bemgba Iortyom, ya ce babu abin da aikin kwamitin ya nuna illa kama-karya da karfa-karfa.

PDP ta ce gwamnan jihar Benuwai ya yi watsi da tsarin mulki da dokar kasa, ya taba dukiyar tsohon Gwamna duk da kotu ta haramta masa yin hakan.

PDP: "Motocin mutanen gari ne"

Jam’iyyar ta ce ‘yan iskan gari ne su ka samu daurin gindin jami’an tsaro da sunan kwamiti, su ka dauke abubuwan hawa a kamfanin Oracle Nig. Ltd.

Ma’aikatan sun shaidawa PDP abubuwan hawan da aka dauka daga garejin na mutanen da ba su da alaka da gwamnati ne da su ka kawo gyara.

...an sace motoci 29

Kara karanta wannan

Da Gaske Wike ‘Karamin Mahaukaci Ne’? Hadimin Atiku Ya Yi Martani Ga Furucin Fayose

Babban Sakataren yada labaran Gwamna Alia, Tersoo Kula ya zargi tsohuwar Gwamnati da sace motoci akalla 29 kafin ta bar mulki a watan Mayu.

Punch ta rahoto Kula ya na cewa motar asibiti da motar yada labarai da ke ofishin Gwamna ba su tsira, dukkansu sun yi kafa a lokacin Samuel Ortom.

Benuwai na cikin inda rigima tayi kamari bayan an yi canjin Gwamnati a karshen Mayun 2023.

Nada Ministocin sabuwar gwamnati

Rahoton da mu ka samu a makon nan ya nuna sunayen wadanda za a tantance a matsayin Ministocin tarayya ya isa hannun hukumomin DSS da EFCC.

Dabarar ta rage ga shugaban kasar ya dauko wadanda su ka san aiki ko dai ya yi wa ‘yan siyasa sakayya, daga ciki har da 'Yan G5 da ake rikici da su a PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng