Zullumi Yayin Da Kotu Ke Shirin Yanke Hukunci Kan Makomar Ministan Buhari, Abubakar Malami

Zullumi Yayin Da Kotu Ke Shirin Yanke Hukunci Kan Makomar Ministan Buhari, Abubakar Malami

  • Ana zargin tsohon ministan Buhari, Abubakar Malami da zargin yin amfani da girman ofishinsa wurin cuta da karfa-karfa don biyan bukatar kansa
  • Dan kasuwa, Cecil Osakwe shi ya maka tsohon ministan gaban kotun inda ya ce Malami ya yi masa karfa-karfa da sa shi ba da kadara da ta kai N130m
  • Alkalin kotun, Oluyemisi Adelaja ya dage sauraran karar zuwa 17 ga watan Oktoba don ba wa Malami damar shiryawa da nemo hanyar kare kansa

FCT, Abuja - Babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraran karar da aka shigar akan tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami kan zargin karfa-karfa.

Kotun, ta bakin Alkalinta, Oluyemisi Adelaja ya dage sauraran karar zuwa 17 ga watan Oktoba don ba wa wanda ake karar daman shiryawa, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yanzu: Kashim Shettima Na Wata Ganawar Sirri Da Shugabannin Majalisar Wakilai a Fadar Gwamnati

Zullumi Yayin Da Kotu Ke Shirin Yanke Hukunci Kan Ministan Buhari, Abubakar Malami
Ana Zargin Tsohon Minista, Abuakar Malami Da Amfani Da Girman Ofishinsa Wurin Yin Karfa-karfa. Hoto: @HisKnowledgeabl.
Asali: Twitter

TheCable ta tattaro cewa wani dan kasuwa, Cecil Osakwe shi ya maka tsohon ministan a gaban kotun.

Zargin da ake yi wa ministan Buhari, Abubakar Malami

A cikin karar, dan kasuwar wanda dillalin filaye ne a Abuja ya ce Malami ya tilasta masa ba wa wata ma'aikaciyar gwamnati, Asabe Waziri gidaje biyu a Maitama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ce Malami ya tilasta masa ba wa Waziri kadarar da ta kai N130m duk da cewa maganar na kotu, inda Cecil ya ce Malami ya shiga tsakani a matsalar kamfaninsa da Waziri.

Wanda ya shigar da karar ya zargi Malami da karfa-karfa

Ya kara da cewa Malami ya umarci jami'an tsaronsa su ci gaba da cin zarafinsa lokacin da ya ke minista.

Ya ce da sanin Malami cewa Waziri ta shafe watanni takwas a gidan kafin kotu ta fitar da ita.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Hasashen Abun da Zai Faru Idan Kotu Ta Tsige Shugaban Kasa Tinubu

Wannan umarnin kotun kuma ya rusa cinikin da ke tsakaninsu da Waziri, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Lauyan Osakwe, Victor Giwa ya koka kan kin halartar Abubakar Malami a farkon fara shari'ar.

Ana Zargin Hadiman Abubakar Malami Kan ‘Karbar Kudi’ Don Masu Laifi Afuwa

A wani labarin, Hukumar EFCC ta kama wasu mutane da ake zargi da karbar kudade don yi wa barayi afuwa.

Mutanen da ake zargin wadanda jami'an ma'aikatar shari'a ne da laifin tattara wadanda aka yi wa afuwan don karbar kudade a hannunsu.

Wata majiya ta bayyana wa hadiman ministan shari'ar cewa mutanen da ke tattara sunayen wadanda za a yi wa afuwan sun shiga hannun hukumar EFCC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.