Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Kan Ƙashe-Kashe a Jihohin Plateau, Da Benue

Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Kan Ƙashe-Kashe a Jihohin Plateau, Da Benue

  • An umarci jami'an tsaro da su zaƙulo masu kitsa hare-haren kwana-kwanan nan da ake kai wa a jihohin Plateau da Benue
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bayar da umarnin yayin da yake Allah wadai da hare-haren ramuwar gayyar da ake kai wa
  • Tinubu ya buƙaci shugabannin ƙauyukan, malaman addini da sarakunan gargajiya da su haɗa hannu wajen samar da zaman lafiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami'an tsaro da su zaƙulo masu kitsa kashe-kashen da ake yi a cikin ƴan kwanakin nan a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau da wasu sassan jihar Benue.

A cewar rahoton NTA News, Tinubu ya bayar da umarnin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dele Alake, ya fitar a ranar Talata, 11 ga watan Yulin 2023.

Kara karanta wannan

Daga Karshe El-Rufai Ya Bayyana Gaskiyar Ma'anar Kalaman Da Ya Yi Kan Hanyar Da Shugaba Tinubu Ya Ci Zabe

Tinubu ya umarci a cafko masu hannu a kashe-kashen jihohin Plateau da Benue
Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da hare-haren Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ƙasar ya yi kira ga ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa da Jama'atu Nasril Islam da ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa da su haɗa hannu waje ɗaya domin aiki tuƙuru wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Shugaba Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Kashe-Kashen

Shugaba Tinubu wanda ya yi Allah wadai da kashe-kashen, ya bayyana hare-haren ramuwar gayyar a matsayin abinda bai kamata ba a tsakanin ƙauyukan na jihohin biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Abin ban takaicin a cikin wannan mummunan tashin hankalin shi ne wata jaririya mai watanni takwas a duniya ta rasa ranta a ƙauyen Farin Lamba na yankin Vwang a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu, a rikicin da ba ta san komai ba a kansa."
"Babban abinda ke biyo bayan tashin hankali shi ne asarar rayukan da basu ji ba basu gani ba."

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bayyana Matakan Da Zai Dauka Wajen Murƙushe Matsalar Tsaro a Mulkinsa

"Domin samun zaman lafiya da ci gaba ana buƙatar haƙuri da juna da yafiya kan kowane irin kuskuren da ake ganin an aikata."

Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci gwamnatocin jihohin biyu da hukumomin bayar da agajin gaggawa da su samar da kayan tallafi ga waɗanda rikicin ya sanya suka rabu da matsugunansu.

Dan Majalisa Ya Bukaci Al'ummar Plateau Su Kare Kansu

A wani labarin na daban kuma, wani ɗan majalisa a jihar Plateau ya buƙaci al'ummar jihar da kare kansu daga hare-haren ƴan bindiga.

Dachung Bagos ya yi kira ga al'ummar jihar da su bi hanyoyin da kundin tsarin mulki domin su kare kansu daga ƴan ta'addan da suka addabi jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng