Sojoji Sun Yi Ram Da Sojan Bogi Da Ya Dade Yana Kwacen Kudade A Hannun Al’umma
- Sojoji sun cafke wani matashin da ke ikirarin shi soja ne a Port Harcourt cikin jihar Rivers da ke cutar mutane
- Wanda ake zargin mai suna Desmond Okehdan asalin jihar Anambra ana zargin shi da cutar mutane da kuma damfara
- Ya bayyana cewa sha'awar aikin soja ne ya sa shi ya ke aikata hakan saboda yadade ya na nema bai samu ba tun 2016
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Rivers - Rundunar soji da ke Port Harcourt a jihar Rivers sun kama wani sojan bogi da ke bayyana kansa matsayin Kofur.
Matashin mai suna Desmond Okeh dan asalin jihar Anambra ana zargin shi da karbar kudade a hannun mutane.
Kakakin rundunar a yanki na 6 da ke Port Harcourt, Ikedichi Iweha shi ya gabatar da sojan bogin ga 'yan jaridu a yau Talata 11 ga watan Yuli.
Sojan bogin ya bayyana yadda ya samu kakin sojojin
Ya ce an kama sojan bogin ne bayan samun bayanan sirri a yankin GRA da ke birnin, Premium Times.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"An kama Desmond Okeh a kusa da bankin New Generation sanye da kakin sojoji da kuma katin shaidar aiki na bogi.
"Ya na sanye da matakin Kofur da kuma lambar aiki, 16N/75/2038 a cikin katin shaidar aiki na bogin."
Wanda ake zargin ya bayyana cewa ya sayi kakin sojojin ne a barikin Kotuko da ke Kaduna, inda ya dinkata a shago.
Inda ya ce ya sayi takalman sojojin daga kasuwar Alaba yayin da ya yi katin bogin kuma a jihar Imo, cewar IRepoteronline
Matashin ya bayyana dalilin aikata hakan
A martanin shi, Okeh ya ce ya na wannan abin ne saboda yadda ya ke son aikin soja bayan rasa damar shiga a lokuta da dama.
Ya ce:
"Tun 2016 na ke neman aikin soja ban samu ba saboda sakamakon jarabawa ta.
"Duk lokacin da nake tare da abokai na da suke aikin, na kan ji kaman nima soja ne."
Kotun A Kano Ta Daure Lauyan Bogi Watanni 15 A Gidan Kaso
A wani labarin, wata kotun shari'ar Musulunci a jihar Kano ta daure wani lauyan bogi watanni 15 a gidan kaso.
Kotun na zargin matashin Zaharaddin Sani Maidoki da laifuka guda biyu da suka hada da cin amana da damfara.
Kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano ta yanke wa matashin daurin watanni 15 a gidan gyaran hali.
Asali: Legit.ng