Dan Majalisar Wakilai Na Jihar Filato Ya Bukaci Al'ummar Jihar Su Kare Kansu Daga Harin 'Yan Bindiga
- Dan Majalisar Wakilai daga jihar Filato, Dachung Bagos, ya buƙaci al'ummar jihar su ƙare kansu daga hare-haren 'yan ta'adda
- Dan majalisar ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-hare a sassan jihar
- Ya ce kundin tsarin mulkin ƙasa ya bai wa kowa damar kare kansa a lokacin da gwamnati ta gaza
Dan Majalisar Tarayya na jihar Filato da ke wakiltar mazaɓar Jos ta Kudu da Jos ta Gabas a Majalisar Wakilai, Dachung Musa Bagos, ya buƙaci al’ummar jihar da su bi hanyoyin da tsarin mulki ya shimfida domin kare kansu.
Ya yi kiran ne a yayin da yake maida martani kan ƙaruwar hare-haren 'yan bindiga da ake samu cikin kwanakin nan a wasu sassa na jihar Filato, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
An bayyana cewa aƙalla mutane 20 ne aka kashe a ƙarshen makon da ya gabata a jihar ta Filato.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa 'yancin kare kansa
Bagos ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin ƙasa ya bai wa kowa 'yancin kare kansa a yayin wata barazana.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce abin takaici ne yadda ɗaruruwan mutane ke ci gaba da mutuwa a kowace rana saboda hare-haren 'yan ta'adda musamman a yankin Mangu, Riyom da Barikin Ladi da ke jihar ta Filato.
Bagos ya ƙara da cewa a yanzu haka mutane da dama ba sa iya noma gonakinsu saboda 'yan ta'addan sun fatattaki mutane daga muhallansu.
Wani ɓangare na jawabinsa na cewa:
“A ranar Asabar ɗin da ta gabata, mutane 12 aka kashe a garin Mangu, sannan kuma a daren jiya an kashe mutane bakwai 'yan mazabata waɗanda suke aikin hakar ma’adinai, wannan aikin dabbancin abin Allah wadai ne.”
Mutane na rayuwa cikin fargaba a jihar Filato
Bagos ya ƙara da cewa mafi yawan mutanen mazaɓarsa na rayuwa ne cikin fargaba saboda hare-haren da 'yan ta'adda ke kawowa a koda yaushe.
Ya jaddada cewa babban nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyar 'yan ƙasa.
A dalilin haka ne ya ce kundin tsarin mulkin ƙasa ya bai wa kowane ɗan ƙasa 'yancin kare kansa a lokacin da gwamnati ta gaza yin hakan.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamnan jihar Caleb Mutfwang, ya kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Mangu bayan harin na ranar Asabar.
Gwamnan jihar Filato ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan sabbin shugabannin tsaro
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto inda gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwan ya bayyana ƙwarin gwiwarsa game da sabbin shugabannin tsaron da Bola Tinubu ya naɗa.
Gwamnan ya ce yana da yaƙinin cewa sabbin shugabannin tsaro na ɓangaren soji da na 'yan sanda za su yi abinda ya dace wajen samar da tsaro.
Asali: Legit.ng