Bidiyon Batsa a WhatsApp ‘Status’ Ya Jawo Gwamnan APC Ya Kori Mai Ba Shi Shawara
- Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris ya bada sanarwar korar Babangida Sarki daga cikin Hadimansa
- Sakataren yada labarai ya fitar da jawabi cewa Hadimin Gwamnan ya yi abin da bai dace ba a WhatsApp
- Ahmed Idris ya yi magana a madadin Gwamnan Kebbi, yana jan-kunne ga masu yin katabora da salula
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kebbi - Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi, ya sallami Mai bada shawara na musamman a harkokin matasa daga mukamin da yake kai.
Rahoton da yake fitowa daga birnin Kebbi shi ne Mai girma Gwamnan ya tsige Alhaji Babangida Sarki ne saboda abin da ya aikata da hannunsa.
Mai ba Gwamnan jihar Kebbi shawara ya wallafa wasu abubuwa na rashin tarbiya a manhajar WhatsApp wanda har ya isa kunnen Nasiru Idris.
CPS ya fitar da jawabi
Da yake bada sanarwar tsige Hadimin, Gwamnan ya ce Babangida Sarki ya ketare iyaka, ya yi abin da ya ci karo da koyar addininsu na musulunci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamna Idris ya nuna wanda aka koran ya zo da abin da ya sabawa tarbiyar mutanen jihar Kebbi, saboda haka ne ya zabi ya koya masa darasi.
Sanarwar ta fito daga ofishin babban sakataren yada labaran Gwamnan Kebbi, Ahmed Idris.
Jaridar Vanguard ta ce Gwamnan ya yi kira ga sauran masu rike da mukaman gwamnati cewa ba zai amince da irin wannan aiki na rashin da'a ba.
Jawabin Ahmed Idris
“Gwamnan ya fusata da wannan abin Allah-wadai, ya ce Hadimin ya ketare iyakokin tarbiyya da tsarin zamantakewar al’umma jihar Kebbi, wanda mafi yawa Musulunci ake bi.
Idris ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa ba za ta cigaba da daukar wannan danten aiki da ke bata halaye da darajar mutane Kebbi."
- Ahmed Idris
Sarki ya ce aikin makiyansa ne
Premium Times ta ce mukarrabin ya daura bidiyon luwadi ne a WhatsApp, hakan ya ya fusata Gwamna wanda yanzu haka ya na Saudi Arabiya.
Sai dai wannan Bawan Allah ya rungumi kaddarar tsige shi daga mukaminsa.
Da aka nemi jin hakikanin abin da ya jawowa Sarki wannan danyen aiki, Daily Nigerian ta rahoto shi yana cewa aikin makiya ne ba kowa ba.
A karshen shekarar bara, mutanen garin Argungu su ka karrama Babangida Sarki bisa kokarin da yake yi na kawo cigaba ga matasan yankin.
Aikin Kwamishinonin jihar Kano
Rahoto ya zo cewa a yau Kwamishinan ma'aikatar lafiya na jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya tare kofa domin ganin masu zuwa a makare.
Shi ma Kwamishinan ilmi, Umar Haruna Doguwa ya kai ziyara zuwa makarantun gwamnati, har ya ba wani hazikin malami kyautar N30, 000.
Asali: Legit.ng