Cire Tallafi: FG Ta Koka Kan Yadda Yawan Shan Mai A Najeriya Ya Ragu Da Lita 18.5m, Ta Fadi Dalili
- Gwamnatin Tarayya ta bayyana yadda amfani da man fetur ke kara raguwa tun bayan cire tallafin man fetur
- Rahoton ya bayyana cewa an samu raguwar da ta kai bambancin lita miliyan 18.5 a wata sakamakon rashin shan mai din
- Kafin cire tallafin ana batar da fiye da lita biliyan 11, amma yanzu ya ragu zuwa lita miliyan 18 da dori
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta koka kan yadda amfani da man fetur ya ragu sosai tun bayan cire tallafin mai a watan Mayu.
Ta ce a farkon wannan shekarar 'yan Najeriya sun sha man fetur da ya kai lita biliyan 11.26, cewar Legit.ng.
Amma tun bayan cire tallafin, yawan shan man fetur din ya ragu zuwa lita miliyan 18.5 a watan Yuni.
Yadda yawan shan mai din ya ragu tun bayan cire tallafi
Kamfanin man fetur a kasar ne ya sanar da haka a ranar Lahadi 9 ga watan Yuli a Abuja, kamar yadda Punch ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce tsakanin watan Janairu zuwa Mayu na wannan shekara, yawan man fetur da 'yan Najeriya suka sha ya tasamma lita biliyan 9.9.
Wannan koma baya da aka samu na yawan shan mai a kasar bai rasa nasaba da cire tallafin mai da Shugaba Tinubu ya yi a watan Mayu, cewar Business Remarks.
Bambancin yawan shan mai din kafin da kuma bayan cire tallafi
Rahoton ya ce tsakanin 1 zuwa 28 ga watan Yuni bayan cire tallafin kenan, an sha man fetur da ya kai lita biliyan 1.36 yayin da a kullum ake shan lita miliyan 48.43 a watan.
Bambancin raguwar shan mai din a wata kafin cire tallafin da kuma bayan cire tallafin ya kai lita miliyan 18.5.
Har ila yau an gano cewa yawan shan man fetur a wasu kwanaki ya kan haura zuwa lita miliyan 100 yayin da wasu kwanaki kuma ya ke raguwa zuwa kasa da lita miliyan 10.
Karyewar Farashi, Rashin Ciniki Da Sauran Matsalolin Da Masu Gidajen Mai Ke Fama Dasu Bayan Cire Tallafi
A wani labarin, tun bayan cire tallafi da Shugaba Tinubu ya yi, 'yan Najeriya suke kokawa akan tsadar mai.
Kafin tsadar mai din an sha fama da karancin mai da aka yi ta korafi tare da zargin masu gidajen mai da boyewa.
A nasu bangaren, masu gidajen mai sun koka kan yadda cire tallafin ke son nakasa musu kasuwa.
Asali: Legit.ng