Yadda Alhazan Kano 9 Suka Barke Da Gudawa A Makkah Bayan Kammala Aikin Hajji, An Bayyana Dalili
- Jami'an lafiya a hukumar alhazai ta sanar da barkewar gudawa a sansanin mahajjatan jihar Kano
- Shugaban jami'an lafiyar, Dakta Usman Galadima shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 9 ga watan Yuli
- Ya ce lamarin ya faru ne bayan alhazan sun ci abincin Takaru saboda sun fi sabawa da shi a gida
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da barkewar gudawa a sansanin mahajjatan jihar Kano a Makkah.
Jami'an kiwon lafiya na hukumar su suka tabbatar da haka ta bakin shugabansu, Dakta Usman Galadima a ranar Lahadi 9 ga watan Yuli.
Ya ce akalla alhazai tara ne suka barke da gudawa dalilin cin abincin Takaru bayan kammala aikin hajji a Saudiyya, Aminiya ta tattaro.
Yadda alhazan suka kamu da gudawa a Makkah
Galadima ya bayyana haka ne a cikin sanarwar da mai yada labaran hukumar, Ibrahim Aliyu ya fitar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar ta kara da cewa lamarin ya faru ne bayan alhazan sun ci wani dambu inda ya ce tuni aka ba su magunguna don shawo kan lamarin.
Ya koka kan yadda alhazai ba sa kiyaye dokokin da aka gindaya musu na cin abincin Takaru barkatai.
Ya ce:
"Alhazan sun dage sai abincin Takaru za su ci saboda sun fi sabawa da shi a gida, wasu kuma suna ci ne saboda guzurinsu ya kare, abin da za su iya siya kenan."
Galadima ya ba wa makuhunta shawarar samar wa alhazan abincin rana
Dakta Galadima ya karyata jita-jitar cewa wannan cutar kwalara ce inda ya ce alhazan su kwantar da hankalinsu a kan bazuwar cutar inda ya roki mahukunta su rinka ba wa alhazan abincin rana don hana su cin abincin Takaru.
A halin yanzu, mahukunta na ba wa alhazan iya abincin safe ne da kuma na dare yayin suke nemo wa kansu abincin rana, cewar Premium Times.
Hajji: Gwamnan Kano Ya Rabawa Alhazan Jiharsa Kyautar Kudi Miliyan 65
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir ya rabawa alhazan jihar Kano kyautar kudi har N65m wa mahajjata fiye da 6,000.
Wannan kyauta a cewar gwamnan an ba da ita ne don alhazan su yi bukukuwan sallah cikin natsuwa.
Gwamnan ya shawarci mahajjatan da su ci gaba da bin dokokin kasar Saudiyya don kare martabar jihar da kasa baki daya.
Asali: Legit.ng