Hukumar NDLEA Tayi Kamen Masu Harkar Kwayoyi, An Yi Ram da Malaman Addini
- Hukumar NDLEA ta yi nasarar kamo wasu gungun mutanen da ke da hannu a fataucin kwayoyi
- Daga cikin wadanda su ka shiga hannu har da masu aiki a coci da kuma wata ma’aikaciyar kamfani
- Mai magana da yawun bakin NDLEA, Femi Babafemi ya sanar da haka a jawabin da ya fitar a Abuja
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Jami’an hukumar NDLEA sun damke wasu mutane hudu da ake zargi su na da hannu a harkar safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.
A rahoton da aka samu daga Daily Trust, an fahimci cewa wadanda su ka shiga hannun ma’aikatan na NDLEA sun hada da ma’aikatan coci.
Har ila yau akwai ma’aikaciyar wani kamfani da wata mata dabam da ake tunani su na taimakawa wajen yawo da mugayen kwayoyi a jihar Delta.
Ana haka kuma rahoto ya zo cewa jami’an hukumar sun auka wani kamfani da ke garin Ogun, su ka kuma yi nasarar cafke kilo 4,560 na kwaya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An yi kame a jihohi 3
Hukumar ta NDLEA ta cafke miyagun kwayoyi ne a garuruwan Legas, Adamawa da kuma Osun.
Mai magana da yawun bakin hukumar yaki da ciniki da fataucin kwayoyin kasar, Femi Babafemi ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar dazu.
Jawabin da aka fitar a Abuja ya ce an cafke ‘yan kwayan fentanyl da ke aiki a Warri a jihar Delta, wata guda bayan kama wasu mutane a jihar Anambra.
Kwanaki Odoh Collins Oguejiofor, Oliver Chigozie Uzoma da su ka shiga hannu a Ogbogwu.
NDLEA: An dade ana yin bincike
Femi Babafemi ya ce sun iya kama wadanda ake zargi ne bayan tsawon lokaci ana binciken shigowar wata kwaya da ta fi Heroine hadari a Duniya.
Ma’aikatan da aka kama su na aiki ne a cocin Christ Mercyland Deliverance Ministries wanda aka fi sani da cocin Mercy City Church a Warri.
Sanarwar hukumar ta bada sunayen ma’aikatan cocin da Adewale Abayomi Ayeni mai shekara 39 da Ebipakebina Appeal mai shekara 41 a Duniya.
Ayeni ya na cikin masu kula da harkar addu’o’i a cocin yayin da Ebipakebina ya ke kula da jigilar bakin cocin daga filin jirgin sama a jihar Delta.
Muhammed Adamu Bulkachuwa a kotu
Kataborar Muhammed Adamu Bulkachuwa ta jawo an fara kira da ayi bincike a kan shi, sai a jiya aka samu labari cewa 'dan siyasar ya kai batun kotu.
Shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/895/2023 ta hada da ‘Yan sanda, DSS da ICPC. Bulkachuwa ya ce doka ta hana binciken abin da aka yi a Majalisa.
Asali: Legit.ng