Tinubu Ya Shilla Kasar Waje, Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Dalili da Lokacin Dawowa

Tinubu Ya Shilla Kasar Waje, Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Dalili da Lokacin Dawowa

  • A ranar Asabar jirgin Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga tashar birnin Abuja zuwa Guinea-Bissau
  • Shugaban Najeriya ya na cikin wadanda za su halarci taron da ECOWAS ta kira a birnin Bissau
  • Dele Alake ya nuna ana kammala taron kungiyar kasashen yammacin Afrikan, Tinubu zai dawo

FCT, Abuja - Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya a ranar Asabar, 9 ga watan Yuli domin halartar taron ECOWAS da za ayi a kasar Guinea-Bissau.

Sanarwar da aka samu daga shafin Twitter a yammacin Juma’a ta tabbatar da shugaban Najeriya zai halarci zamansa na farko a taron ECOWAS.

Shugabanni da gwamnatocin kasashen da ke karkashin kungiyar ECOWAS na yammacin Afrika za su yi zama a birnin Bissau a ranar Lahadi.

Tinubu
Bola Tinubu a Legas Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter

Jawabin da Mai ba shugaban Najeriyan ya fitar ya nuna taron da za ayi wannan karo zai fi maida hankali a kan wasu muhimman abububuwa uku.

Kara karanta wannan

TETFund: Bayan Shekaru 10, Sababbin ‘Yan Majalisa Za Su Binciki Gwamnatin Jonathan

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tattaunawar za ta shafi batun saukaka kasuwanci tsakanin kasashen da ke yammacin nahiyar.

Abubuwan da za a tattauna a taron

Alake ya ce zaman da za ayi zai duba rahoton tsaro da wasu kasashe ke fuskanta da shirin samar da kudi daya domin duka kasashen yankin.

ECOWAS ta na yunkurin inganta kasuwanci ta yadda za a iya yawo da kaya daga birnin Abidjan zuwa Legas ba tare da kakaba wani kaidi ba.

A wajen wannan zama ne shugabannin kungiyar ta ECOWAS za su tattauna a kan shirin mika mulki a kasashen Mali, Burkina Faso da Guinea.

Tinubu zai taka kasar Afrika

Leadership ta ce Guinea-Bissau za ta zama kasar Afrikar farko da Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara tun bayan zamansa shugaban Najeriya.

Masu ba shugaban kasar shawara a kan manufofin gwamnati da kuma wasu manyan jami’ai za su yi masa rakiya wannan karo zuwa Bissau.

Kara karanta wannan

Asalin Abin da Ya Kai Ni Wajen Tinubu a Aso Rock – ‘Dan Takaran Shugaban Kasa a PDP

Da zarar an kammala taron, jirgin fadar shugaban Najeriyan zai kamo hanyar birnin Abuja.

Bola Tinubu a Faris

A karshen watan Yuni aka ji labari Mai girma Bola Tinubu ya ziyarci Faransa, daga nan ya shafe wasu kwanaki a Landan a Ingila kafin ya dawo gida.

Emmanuel Macron ya zama mai masaukin bakin shugabannin da su ka je taron. Daga baya Tinubu ya hadu da 'yan Najeriya da su ke zaune a Faris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng