Tinubu Ya Yi Abin da Ya Gagari Buhari, Ya Sasanta Rikicin Hukumomi 2 Cikin Wata 1

Tinubu Ya Yi Abin da Ya Gagari Buhari, Ya Sasanta Rikicin Hukumomi 2 Cikin Wata 1

  • Ana samun rashin jituwa a gwamnatin tarayya tsakanin wasu hukumomi saboda dalilai da-dama
  • Alal misali, sabani ya na yawon bata ayyukan ma’aikatan NUPRC da NMDPRA wajen harkokin mai
  • Bola Tinubu ya kama hanyar dinke barakar, gwamnatin tarayya ta gindaya kowa aikinsa a doka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Bayan kusa wata daya a ofis, Bola Ahmed Tinubu ya fara kokarin shawo kan rigimar da ake yi a gwamnatin tarayya wanda ya gada da ya hau mulki.

Kamar yadda rahoto ya zo a This Day, babu jituwa tsakanin jami’an hukumar NUPRC da NMDPRA, ana yawan samun sabani tsakanin ma’aikatan wajen aiki.

A wata takarda da ta fito kwanan nan, Mai girma shugaban Najeriya na neman shatawa kowa layi domin ma’aikatan hukumomin man su san matsayinsu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dala: Gwamnati Ta Janye Ƙarar da ta Haramtawa EFCC Binciken Ganduje

Tinubu
Bola Ahmed Tinubu a wajen taro Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Dokar PIA ta haifar da matsala

Bola Tunubu zai raba fadan nan ne kafin ayi wa dokar PIA kwaskwarima a majalisar tarayya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Takardar da fadar shugaban kasa ta aikawa ma’aikatar shari’a ta nuna za a fayyace NUPRC da NMDPRA ayyukansu domin su daina yi wa junansu shisshigi.

Kafin Muhammadu Buhari ya bar kujerar mulki a Mayu, ya umarci NUPRC ta rika sa ido a kan duk wasu tashoshin da ake fita da danyen mai daga Najeriya.

Buhari wanda shi ne babban Ministan harkar mai a loacin, ya gargadi sauran hukumomi musamman NMDPRA cewa babu ruwanta da tashoshin mai.

Rigimar NMDPRA da NUPRC ta dawo

Rahoton ya ce kafin jan-kunne ya kai ga ma’aikatan NMDPRA, har rikici ya barke tsakaninsu da takwarorinsu kan zargin ExxonMobil da daukar danyen mai.

Hukumar da aka sani a baya da DPR, ta zargi kamfanin ExxonMobil da taba arzikin Najeriya ba tare da ka’ida ba, NMDPRA, ta na ikirarin hurumia fannin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Ƙasa da Sakatare a Villa

Domin ganin an daina samun abin kunyan nan, The Cable ta ce Shugaba Tinubu ya bukaci ayi amfani da zane domin a ankarar da kowace hukuma aikinta.

...Yunkurin gwamnatin Tinubu

Sabon shugaban kasar ya yarda cewa dokar da aka fito da ita ta taimaka wajen jawo rashin fahimtar, ya nanata cewa NUPRC ce mai kula da harkar ciniki.

Game da ayyukan da su ka shafi sa ido da kuma kwarewa, nauyin ya rataya ne ha hukumar NMDPRA. Gwamnati ta bukaci ma’aikata su fahimci haka.

Farashin fetur zai tashi?

A baya an samu rahoto cewa kungiyar OPEC na shirin rage adadin danyen man da kasashenta su ke hakowa a kullum bayan matsin lamba daga Saudi Arabiya.

Idan Kasar Saudi ta yi nasarar tashin kudin ganga, shakka babu litar fetur ya kara tsada, a halin yanzu farashin fetur bai wuce N515 zuwa N540 a duk Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng