Shugaba Tinubu Ya Tura Sunayen Sabbin Hafsoshin Tsaro Zuwa Majalisa

Shugaba Tinubu Ya Tura Sunayen Sabbin Hafsoshin Tsaro Zuwa Majalisa

  • Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya buƙaci majalisar tarayya ta tabbatar da hafsoshin tsaron da ya naɗa a hukumance
  • Hakan na kunshe a wata wasiƙa da shugaban ya aike majalisa kuma kakaki, Tajudeen Abbas ya karanta a zaman yau Talata
  • Tinubu ya roƙi 'yan majalisar da su hanzarta wajen tabbatar da naɗa hafsoshin tsaron kamar yadda kundin doka ya tanada

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zamfara state - A hukumance shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tura wasiƙa zuwa ga majalisar tarayya, inda ya sanar da su cewa ya yi sabbin naɗe-naɗe.

Shugaban kasan ya tura sunayen sabbin hafsoshin tsaron da ya naɗa yana mai rokon majalisun su tantance tare da tabbatar da su, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Tura Sunayen Sabbin Hafsoshin Tsaro Zuwa Majalisa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A wata wasiƙa mai ɗauke da adireshin kakakin majalisar wakilan tarayya, shugaban ƙasa ya roƙi 'yan majalisun su hanzarta tabbatar da naɗin babban hafsan tsaro (CDS) da sauran hafsoshi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Ƙasa da Sakatare a Villa

Idan zaku iya tuna wa, shugaba Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin tsaro a Najeriya a daidai lokacin majalisar tarayya tana hutun babbar sallah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin sabbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya nemi amincewar majalisa

Sabbin manyan hafsoshin tsaron da su ke jiran tabbatarwa a majalisar tarayya sun haɗa da:

1. Manjo Janar C.G Musa - Babban hafsan tsaron Najeriya (CDS)

2. Manjo T. A Lagbaja - Shugaban rundunar sojin ƙasa ta Najeriya

3. Rear Admirral E. A Ogalla - Shugaban hukumar sojin ruwa ta Najeriya

4. Air Vice Marshal H.B Abubakar - Shugaban hukumar sajin saman Najeriya.

A cikin wasiƙar, shugaba Tinubu ya yi bayanin cewa wannan bukata ta yi daidai da tanadin sashi na 18(1) da ke kundin dokar sojin tarayyan Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tuni sabbin hafsoshin tsaron da shugaba Tinubu suka kama aiki a ofisoshinsu daban-daban.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP 2 a Aso Villa

Shugaba Tinubu Ya Gana da Tsohon Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose a Aso Villa

A wani rahoton na daban shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (GCFR) ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a Villa.

A jawabinsa bayan gana wa da shugaban kasa, Fayose ya jaddada cewa ba bu wani shirin zai fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262