Kotu Ta Bayar Da Belin Korarren Dan Sanda Abba Kyari Kan Miliyan 50
- Babbar kotun Abuja ta ba da belin dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP Abba Kyari
- An bayar da belin Kyari kan kudi naira miliyan 50 tare da mutane biyu da za su tsaya masa
- Mai shari'a James Omotosho ne ya bayar da belin a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli
Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin dakataccen DCP Abba Kyari kan kudi naira miliyan 50 bisa tuhumar da ake yi masu shi da yan uwansa biyu kan zargin kin bayyanawa hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA kadarorinsu.
Hukumar NDLEA ta shigar da tuhume-tuhume 24 masu lamba FHC/ABJ/CR/408/2022 a kan Kyari da yan uwansa guda biyu – Mohammed Baba Kyari da Ali Kyari – wadanda aka gurfanar da su a kansu a watan da ya gabata.
Abba Kyari zai biya miliyan 50 da mutane biyu da za su tsaya masa
Da yake zartar da hukunci a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, Justis James Omotosho ya bayar da beli ga Abba Kyari bisa sharadin biyan naira miliyan 50 tare da mutane biyu da za su tsaya masa, rahoton The Nation.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Justice Omotosho ya kara da cewar ya zama dole wadanda za su tsaya masa su zamana sun mallaki kadarar da ta kai naira miliyan 25 karkashin ikon shari’a da sauran sharudda.
Alkalin ya riki cewa, ko da Abba Kyari ya cika sharuddan belin, yarda da sakinsa ya ta’allaka ne a kan ci gaba a shari’ar da ake yi da shi kan wasu zarge-zarge hudu da ake yi masa na hannu a safarar miyagun kwayoyi.
Sau biyu ana hana shi beli a sauran shari’ar da ake yi da shi a gaban Justis Emeka Nwite, shima a babbar kotun tarayya, Abuja.
Justis Omotosho ya ba da belin yan uwansa biyu a baya.
An hana yan jarida da lauyoyi shiga wajen sauraron shari'ar Abba Kyari
A gefe guda, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kotu ta hana ‘yan jaridu da lauyoyi da kuma sauran jama’a shiga cikin kotun da ake ci gaba da sauraren karar Abba Kyari da ake zargi da safarar kwayoyi, a ranar Talata 16 ga watan Mayu a kotun dake zamanta a Abuja.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ba da wannan sanarwa bayan lauyan dake kare Hukumar Hana Sha da Fataucin Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) Mista Joseph ya shigar da korafi don kare masu ba da shaida a kotu.
Asali: Legit.ng