Bidiyon Dala: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Aika Sammaci Ga Ganduje
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta aika takardar gayyata ga tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje
- Hukumar PCACC ta ce za ta yi wa Ganduje tambayoyi a kan bidiyonsa da ya yadu a shekarun baya inda aka zarge shi da karbar cin hanci daga yan kwangila
- A halin da ake ciki, Muhuyi Magaji Rimingado, shugaban hukunmar PCACC, ya tabbatar da cewar bidiyon na gaske ne ba na bogi ba
Kano - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano (PCACC) ta aika sammaci ga tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, don amsa tambayoyi a kan bidiyon dala.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wata jaridar yanar gizo ce ta fara sakin bidiyon a 2017, inda ta kara da cewar an zargi tsohon gwamnan da karbar cin hanci daga wajen yan kwangila.
A cikin bidiyoyin, an gano Ganduje yana karbar daloli sannan yana cusawa a cikin farin babbanrigarsa.
Sai dai kuma tsohon gwamnan ya karyata zargin sannan ya yi ikirarin cewa bidiyon na bogi ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar PCACC ta aika takardar gayyata ga Ganduje don ya amsa tambayoyi, Rimingado
Muhuyi Magaji Rimingado, shugaban hukunmar PCACC, a wani taron wayar da kan jama'a kan yaki da rashawa a Kano, ya bayyana cewa an tabbatar da bidiyon na gaske ne.
Da yake magana a kan bidiyon a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, Rimingado ya ce an gayyaci tsohon gwamnan domin ya amsa tambayoyi.
Binciken kimiyya ya nuna bidiyon dalar Ganduje gaskiya ne, Rimingado
A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta ce binciken kimiyya ya tabbatar da cewar bidiyon dala na tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba na bogi bane.
Bidiyon Dala: Hukumar Yaƙi Da Rashawa ta Kano Ta Bayyana Yadda Bidiyon Ya Taba Ƙimar Kano a Idon Duniya
Da yake magana a wani taron tattaunawa kan yaki da rashawa a Kano a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya tabbatar da sahihancin bidiyoyin tsohon gwamnan.
Ya ce hukumarsa ta fara bincike a 2018 amma bata yi nisa ba saboda Ganduje, wanda ya kasance gwamna a wancan lokacin yana da rigar kariya.
Asali: Legit.ng