Rundunar Sojin Sama Ta Kashe Yan Ta’addan ISWAP Masu Yawan Gaske a Jihar Borno
- Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun yi gagarumin nasara a kan mayakan kungiyar ta'addanci da suka addabi yankin arewa maso gabas
- Sojojin sun yi yayyafi wuta a kan mayakan ISWAP da dama a yankin Marte da ke jihar Borno
- An kai farmakin ne bayan binciken sirri ya nuna akwai yan ta'adda masu yawan gaske a yankin
Borno - Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun halaka mayakan kungiyar ta'addanci na ISWAP da dama a wani mummunan hari da suka kai masu ta sama a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli.
Zagazola Makama ya rahoto cewa rundunar sojin saman ta yi wa mayakan yayyafin wuta ne a kusa da Marte, hedkwatar wata karamar hukuma a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Dakarun Operation Hadin Kai sun ragargaji yan ISWAP ta sama
An kashe yan ta'addan ne a wani farmaki da rundunar sojin Operation Hadin Kai suka kai ta sama a Tumbum SHITTU.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwararren masanin lamarin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, wanda ya bayyana haka a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, ya ce an aiwatar da farmakin sojin ne bayan bincike ya nuna akwai tarin yan ta'addan a yankin.
Wata majiyar sirri da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:
"An kai harin saman ne da nufin kawar da mabuyan yan ISWAP."
Gwamnatin Babagana Zulum ta sha alwashin daukar mummunan mataki a kan mayakan ISWAP
A wani labari na daban, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya nuna bakin cikinsa a kisan gillar da mayakan ISWAP suka yi wa wasu manoma takwas a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno.
Fashin Fadar Sarkin Minna: Bincike Ya Nuna Da Dan Gari Aka Ci Gari, An Tabbatar Da Mutuwar Dogarawa 2
An dai farmaki manoman ne garuruwan Shuwarin, Tomsu Ngamdu, Baram Karauwa da Muna a ranar Alhamis, yayin da suke tsaka da aiki a gonakinsu
Zulum wanda ya ziyarci Mafa, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
An kashe kasurgumin dan bindigan Zamfar, Dogo Gudali
A gefe guda, mun ji cewa kasurgumin shugaban yan bindiga, Dogo Gudali, wanda ya addabi al'umma musamman a jihar Zamfara ya kwanta dama
Gudali ya hadu da ajalinsa ne bayan wasu mambobin kungiyarsa na ta'addanci sun dana bam da nufin farmakar dakarun sojoji.
Asali: Legit.ng