“Ina Kashe Kasa Da N2k Wajen Cika Tankina”: Dan Najeriya Ya Mayar Da Motarsa Zuwa Mai Amfani da Gas
- Wani matashi dan Najeriya ya yi wani bidiyo don nunawa mutane yadda motarsa ke amfani da iskar gas kuma bai damu da tsadar man fetur ba
- Tankin motar na a gaban motar ne sabanin motoci masu amfani da man fetur da tankinsu ke baya
- Yan Najeriya da suka ga ya biya kasa da N2,000 don cika tankinsa sun nemi sanin yadda za su iya sauya nasu injinan
Wani matashi dan Najeriya ya nunawa mutane yadda yake amfani da motarsa ba tare da damuwa da tsadar mai ba.
Da yake baje kolin injin dinsa wanda aka sauya zuwa mai amfani da iskar gas, mutumin ya dauki motar zuwa gidan mai domin siyan gas. Ya bayyana cewa ba zai kashe fiye da N2000 ba wajen cika tankin.
Mai motar ya ce abokinsa wanda ya nuna masa hanya ya kashe N60,000 wajen sauya injin din.
Bayan an cika tankin motar, N1,800 kacal mutumin ya biya. Cikin kasa da mintuna uku aka cika tankin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cikin wani bidiyon, mutumin ya bayyana cewa iskar gas bai da hatsari ga injin motar.
Ya kamata a lura cewa iskar gas da ake sanya wa mota 'Compressed Natural Gas (CNG)' ne kuma ya banbanta da sanannen gas din LPG.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Phellype ta ce:
"Ya kamata ku daina bari Tinubu yana jin karin bayani."
Jide Jimo Mokwenye ya ce:
"Wato da Tinubu bai hau karagar mulki ba ba za mu samu wannan karin bayanin ba ko???"
BB ya ce:
"Kwanan nan gas zai yi tsada."
olusolataiwo593 ya ce:
"Ina kwana, don Allah a ina zan iya sauya motata kirar toyota camry 2000 don amfani da CNG a lagas?"
kelly ta ce:
"Yan Najeriya dole mu rayu ta kowani hali."
OLUWASOGO BEN OBITAYO:
"Dan Allah faaa ina bukatar sauya nawa."
joejoe_12:
"Nawa ake sauya shi?"
Matashi ya mayar da janaretonsa zuwa mai amfani da gas
A wani labari na daban, mun ji cewa yayin da farshin man fetur ya yi tashin gauron zabi, wasu yan Najeriya suna neman hanyoyin da za su dunga tayar da janaretonsu.
Wani bidiyo da Orilomo ya wallafa a TikTok ya nuna wani janareto yana aiki da tukunyar gas ba tare da tangarda ba.
Asali: Legit.ng