Kotu Ta Tsare Matashi Mai Fenti Bisa Zargin Satar Jita Da Makirfo 2 A Majami'a, Ya Musanta Zargin

Kotu Ta Tsare Matashi Mai Fenti Bisa Zargin Satar Jita Da Makirfo 2 A Majami'a, Ya Musanta Zargin

  • Kotun da ke zamanta a Dei-Dei ta tsare wani matashi da ake zargin wuce gona da iri da kuma yin sata
  • Ana zargin Darlington Chibundu da satar jita da kuma makirfon guda biyu a wata majami'a da ke Dutse Alhaji a Abuja
  • Yayin da Chibundu ya musanta zargin da ake masa, Alkalin kotun ya ba da umarnin tsare shi a gidan kaso

FCT, Abuja - Wata kotu da ke zamanta a Dei-Dei a cikin birnin Abuja ta tsare wani matashi bisa zargin satar jita a majami'a.

Wanda ake zargin Darlington Chibundu mai shekaru 39 ya kuma saci makirfo guda biyu da jimillarsu duka ya kai N210,000.

Kotu Ta Tsare Mai Fenti Kan Zargin Satar Jita Da Makirfo 2 A Majami'a
Matashin Ya Saci Kayan Da Kudinsu Ya Kai N210,000. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Kotun na tuhumar Chibundu da wuce gona da iri da kuma yin sata, Daily Post ta tattaro.

Yadda matashin ya saci jita da makirfo a cikin majami'a

Kara karanta wannan

Borno: EFCC Ta Kama Wani Da Ake Zargi Da Handame Dukiyar Magada Har 12m

Mista Chibundu da ke rayuwa a yankin Koro a Dutse Alhaji da ke Abuja ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko, mai gabatar da kara Charity Nwaosu ta fadawa kotu cewar Chibundu ya aikata laifin ne a ranar 29 ga watan Yuni.

Ta ce wani mai suna Francis Orji na majami'ar Dutse Makaranta ne ya kawo rahoton faruwar lamarin a ranar 29 ga watan Yuni a ofishin 'yan sanda na Dutse Alhaji.

Matashin ya musanta zargin da ake masa na sata da wuce gona da iri

Ta kara da cewa kudin jitar ya kai N70,000 yayin da kudin makirfon din guda biyu suka kai N140,000, cewar Pulse.

Ta ce yayin binciken 'yan sanda wanda ake zargin ya tabbatar da aikata hakan inda aka samu kayayyakin a wurinshi.

Yayin da Chibundu ya musanta zargin da ake masa, Alkalin kotun, Saminu Suleiman ya umarci tsare Chibundu a gidan kaso da ke Suleja.

Kara karanta wannan

A Maimakon Kujerar Minista, Shehu Sani Ya Fadi Abin da Ya Dace da Tsofaffin Gwamnoni

Alkalin kotun har ila yau, ya dage ci gaba da sauraran karar zuwa 8 ga watan Agusta.

Kotu Ta Tsare Matashi Bisa Zargin Satar Jaririya Mai Watanni 2

A wani labari, wata kotu ta tsare matashi bisa zargin satar jaririya mai watanni biyu a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa.

Matashin Kingsley Solomon ya yi ikirarin cewa ba niyyar sata ya yi hasalima jaririyar shi ne mahaifinta.

A ranar 23 ga watan Yuni Solomon ya naushi Joy wacce ita ce mahaifiyar jaririyar a fuska don dauke ta daga gare ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.