Hajjin 2023: Maniyyaciiyar Jihar Kano Ta Rasu A Saudiyya Bayan Fama Da Jinya
- Hukumar Alhazan jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar daya daga cikin mahajjatan jihar a Makkah bayan fama da jinya
- Marigayiyar mai suna Hadiza Isma'il ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya a birnin Makkah da ke Saudiyya a ranar Litinin 3 ga watan Yuli
- Babban daraktan hukumar a jihar, Alhaji Laminu Rabiu ya mika sakon ta'aziya ga iyalanta a madadin gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf
Jihar Kano - Daya daga cikin mahajjatan jihar Kano mai suna Hadiza Isma'il ta rasu yayin aikin hajji a Makkah da ke Saudiyya.
Marigayiyar ta rasu ne a ranar Litinin 3 ga watan Yuli da misalin karfe 3:15 na yamma agogon kasar Saudiyya bayan fama da jinya.
Yadda maniyyaciyar Kano ta rasu a Saudiyya
Matar mai shekaru 58 ta kamu da zazzabi yayin da aka yi jinyarta a asibitin hukumar alhazai, cewar Punch.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga bisani da abin ya ki ci ya ki cinyewa sai aka mayar da ita asibitin Sarki Abdulaziz da ke birnin Makkah inda Allah ya karbi rayuwarta.
Tuni aka binne ta a birnin Makkah bayan an yi sallar jana'izarta a masallacin Ka'aba.
Daraktan hukumar ya mika sakon jaje a madadin Abba Gida Gida
Babban daraktan hukumar alhazai ta jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu Danbappa ya tabbatar da rasuwar matar, cewar rahotanni.
Danbappa yayin tabbatar da labarin ya mika ta'aziya ga iyalan marigayiyar a madadin gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Ya yi addu'ar ubangiji ya gafarta mata, ya kuma ba wa iyalanta hakurin jure wannan babban rashi.
Mahajjata da dama sun rasu yayin aikin bana kamar yadda maniyyaciya daga birnin Tarayya Abuja Hajiya Amina Yunusa ta rasu a Saudiyya yayin aikin hajji.
Hajjin 2023: Maniyaciyyar Abuja Ta Riga Mu Gidan Gaskiya A Saudiyya
A wani labarin, daya daga cikin maniyyata aikin hajji a Abuja ta riga mu gidan gaskiya a Saudiyya.
Hukumar alhazan birnin Tarayyar ne ta bayyana da haka ta bakin babban daraktan, Malam Abubakar Evuti.
Marigayiyar mai suna Hajiya Amina Yunusa ta rasu ne a Makka bayan fama da jinya.
Asali: Legit.ng