Kano: Kotu Ta Umarci Tsare Tsohon Kwamishinan Ganduje Har Kwanaki 12 Kan Zargin Badakalar N1bn

Kano: Kotu Ta Umarci Tsare Tsohon Kwamishinan Ganduje Har Kwanaki 12 Kan Zargin Badakalar N1bn

  • Kotun majistare a Kano ta ba da umarnin ci gaba da tsare tsohon kwamishinan ayyuka a tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje
  • Alkalin kotun, Tijjani Minjibir shi ya ba da wannan umarni na ci gaba da tsare Idris Wada har tsawon kwanaki 12 don bincike
  • An kama tsohon kwamishinan tare da wasu mutane guda hudu da ake zargin su da badakar makudan kudaden jama’a a jihar

Jihar Kano – Kotun Majistare da ke jihar Kano ta ba da dama wa hukumar yaki da cin hanci ta jihar da ta ci gaba da tsare Idris Wada har tsawon kwanaki 12.

Tsohon kwamishinan a tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje, Idris Wada ana zarginshi da wasu mutane da badakalar N1bn.

Kotu ta ba da umarnin ci gaba da tsare tsohon kwamishina a jihar Kano
Ana Zargin Tsohon Kwamishinan Da Wawure Makudan Kudade. Hoto: Legit.ng Hausa.
Asali: Facebook

Alkalin kotun, Tijjani Minjibir shi ya ba da wannan umarni na ci gaba da tsare tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Channels TV ta tattaro.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Gangwaje Alhazan Jihar Kano, Ya Ba Su Kyautar Miliyan 65

Hukuncin kotun ta ba wa hukumar damar ci gaba da tsare tsohon kwamishinan

Wannan na zuwa ne bayan kama tsohon kwamishinan da sakataren din-din-din da kuma daraktoci 3 a wasu ma’aikatun jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan hukuncin kotun zai ba wa hukumar damar ci gaba da tsare Wada don yin bincike da tambayoyi.

Hukuncin ya biyo bayan shaidu da hukumar yaki da cin hanci ta gabatar don ba su karin lokaci na tambayoyi.

Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji ya tabbatar da kama mutanen inda ya jaddada himmatuwar hukumar wurin bankado gaskiya duk inda take.

Muhuyi ya bayyana girman laifin da suka aikata na cin hanci

Ya ce:

“Mun dauki matakin kama Alhaji Idris Wada, tsohon kwamishinan ayyuka da wasu mutane hudu.
“Wannan mataki ne na nuna cewa an inganta ma’aikatu tare da tsaftace su don yin aiki yadda ya kamata.”

Kara karanta wannan

Ana Wata Ga Wata: An Kama Kwamishinan Ganduje Kan Badakalar Biliyan 1

Magaji ya kara da cewa zargin da ake yi wa mutanen ba kadan ba ne, don haka ana bukatar yin bincike sosai, cewar Vanguard.

Ya ce:

“Zargin cin hanci da rashawa a wadannan ma’aikatu ba kadan ba ne don haka ana bukatar bincike mai zurfi da kuma shaidu don tabbatarwa.

Kano: Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kama Kwamishinan Ganduje Da Wasu Kan Badakalar N1bn

A wani labarin, Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano ta kama tsohon kwamishina a gwamnatin Ganduje kan badakar N1bn.

Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji ya sha alwashin kawo karshen cin hanci da rashawa a jihar.

Tsohon kwamishinan an kama shi ne tare wasu mutane guda hudu da ake zargin da wawure N1bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.