Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wakilan Bankin Amurka a Villa

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wakilan Bankin Amurka a Villa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara ƙarfafa shirye-shiryen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan ta yadda zai tsayu da ƙafafunsa
  • Ya tabbatar da hakan a ranar Talata, 4 ga watan Yuli, lokacin da ya karɓi baƙuncin wakilan bankin Amurka domin wani muhimmin taro a Villa
  • Wakilan na bankin Amurka suna a ƙarƙashin jagorancin shugaban bankin na ƙasa na yankin Saharar Afirika. Mr Bernard Mensah

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Aso Villa, FCT - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan da ƙara haɓɓaka dangantakar da ke tsakanin ƙasar nan da ƙasashen waje.

A ranar Talata, 4 ga watan Yuli, Shugaba Tinubu ya sanya labule da wakilan bankin Amurka a fadar shugaban ƙasa da ke a Aso Rock Villa.

Shugaba Tinubu ya gana da wakilan bankin Amurka
Shugaba Tinubu ya sanya labule da wakilan bankin Amurka Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, wakilan bankin na Amurka sun zo ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban bankin na ƙasa na yankin Saharar Afirika, Mr Bernard Mensah.

Kara karanta wannan

Rayukan Bayin Allah Da Dama Sun Salwanta a Wani Sabon Rikicin Kabilanci a Jihar Arewa

Sauran manyan ƙusoshin bankin na Amurka da suka halarci zaman sun haɗa da shugabar yankin Saharar Afirika, Mrs Yvonne Ike Fasinro da shugaban fannin zuba jari na yankin Saharar Afirika, Mr Chuba Ezenwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Me suka tattauna a wajen taron?

Har yanzu dai cikakkun bayani kan tattaunawar ta su basu fito ba, amma alamu masu ƙarfi na nuni da cewa zaman na su zai yi ƙoƙarin samar da hanyoyin da za su taimaka wajen dawo da tattalin arziƙin ƙasar nan akan turba.

Tun bayan dawowarsa daga hutun Sallah da ya yi a birnin Legas, Shugaba Tinubu ƴa duƙufa aiki gadan-gadan wajen tafiyar da mulkin ƙasar nan, inda ya gana da mutane masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban.

Shugaba Tinubu Ƴa Gana Da Hafsoshin Tsaro

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinibu ya gana da hafsoshin tsaron ƙasar nan da mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Mallam Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

"Allah Ba Zai Ɗora Mana Abinda Ba Zamu Iya Ba" Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali a Masallacin Idi

Shugaban ƙasar wanda ya yi ganawar farko da hafsoshin tsaron tun bayan da ya naɗa su, na son zaƙulo hanyoyin magance matsalolin tsaron da ƙasar nan ke ci gaba da fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng