Dan Jaridan Najeriya Ya Lissafo Kura-kurai 6 Da Buhari Ya Yi, Ya Gargadi Tinubu Akan Fadawa Tarkon

Dan Jaridan Najeriya Ya Lissafo Kura-kurai 6 Da Buhari Ya Yi, Ya Gargadi Tinubu Akan Fadawa Tarkon

  • Wani dan jarida a Najeriya ya gargadi Shugaba Bola Tinubu da kada ya yi kuskuren da Buhari ya yi
  • Mayowa Tijani wanda ke aiki da The Cable ya ce akwai kura-kurai shida da Buhari ya yi a lokacin mulkinsa
  • Ya lissafo kura-kuren inda ya ce idan Tinubu ya kuma aikata kurakuran zai lalata gwamnatinsa kamar na Buhari

Wani dan jarida a Najeriya ya ba wa Shugaba Bola Tinubu shawara akan kura-kuran tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Dan jaridar mai suna Mayowa Tijani wanda ke aiki da TheCable ya ce dole Tinubu ya kaucewa wadannan kura-kurai 6 da Buhari ya yi a mulkinsa.

Dan jarida a Najeriya ya lissafo kurakurai 6 da Buhari ya yi, ya gargadi Tinubu
Shugaba Bola Tinubu Da Buhari. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/ Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro kura-kuren da dan jarida Tijani ya lissafo kamar haka:

1. Rashin cire tallafin mai

Mayowa ya ce rashin cire tallafin mai shi ne babban kuskuren da Buhari ya yi tun farkon karbar mulki a 2015.

Kara karanta wannan

'Rashin Da'a Ga Buhari': Tajudeen Abbas Ya Barranta Kansa Da Kalaman Hadiminsa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce Buhari ya ki jin shawarar tsohon ministan harkokin mai, Ibe Kachikwu tun farko inda ya yi ta wasa da arzikin kasar wurin biyan kudin tallafi.

Ya yabawa Tinubu kan cire tallafin amma ya ce shugaban bai samar da wani tsari na rage radadin hakan ba.

2. Rike matatun man Najeriya

Mayowa ya ce kuskure na biyu da Buhari ya yi shi ne kashe makudan kudade akan wadannan lalatattun matatar man fetur da ba su tsinana komai ba.

Ya ce abin da ya kamata shi ne a siyar da wadannan matatun mai wa 'yan kasuwa don inganta su.

3. Katsalandan a harkokin shari'a

Tijani ya ce duk tsawon shekarun da Buhari ya yi akan mulki ya na bin umarnin kotu idan sun yi masa dadi, idan kuma aka samu sabanin haka to sai ya yi fatali da umarnin.

Kara karanta wannan

Abu namu: Buhari ya tura wa Tinubu sunan wanda yake so a ba Minista daga Katsina

Ya ce ya lura Shugaba Tinubu ya kama hanyar yin wannan babban kuskure na yi wa shari'a katsalandan.

Ya bada misali yayin jawabin shugaban a ranar 12 ga watan Yuni kamar haka:

"Ya zama dole ku sani cewa ba za mu lamunci duk wata umarnin kotu da take kawo cikas ga ci gaban dimukradiyya ba."

4. Rashin tsari a tattalin arziki

Ya bayyana yadda Buhari ya gagara fitar da ministocinsa har tsawon wata shida a 2015, wanda hakan yasa masu zuba hannun jari suka bar kasar a wannan lokaci.

Ya ce Tinubu na garajen fada wa wannan matsalar yayin da ya shafe kwanaki 37 babu ministan kudi da kuma gwamnan babban bankin Najeriya.

5. Soyayyar makanta ga shugabanni

So na makanta da ake wa shugabanni ba karamar matsala ba ce kamar yadda Buhari ya fuskanta, hakan ba ya gina kasa.

Ya ce:

"Makwanni biyu da suka wuce, Ngozi Okonjo-Iweala ta wallafa wasu hotuna yayin wani taro a Faransa, cikin mintuna magoya bayan Tinubu da Peter Obi suka fara fadan wasu abubuwa na takaici.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Bar Mahaifarsa Ta Daura, Cikakken Bayani Ya Bayyana

"Wannan shi ne matsalar Buhari, magana tsakanin 'su' da 'mu' ya kamata Tinubu ya kauce masa, ba abu ne mai kyau ba, ku wayar da kan magoya bayanku na intanet."

6. Almubazzaranci da dukiyoyin jama'a

Tinubu ya dauki wasu matakai da suke kuntatawa 'yan Najeriya, kuma sun yi imanin hakan zai rage yawan kashe kudade.

Yawan kashe kudade a gwamnatin Buhari ya yi yawa, bai kamata Tinubu ya zama shugaban kasa mai almubazzaranci ba, na kara fada, kada ka zama Buhari.

Tinubu Ya Gana Da Buhari A Birnin Landan, An Bayyana Dalilin Haduwar

A wani labarin, shugaban kasa, Bola Tinubu ya gana da tsohon shugaban kasa Buhari a London.

Yayin tattara wannan rahoto babu wanda ya san dalilin haduwar tasu da kuma abubuwan da suka tattauna.

Sai dai hadiman shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sun wallafa hotunansu a kafar sadarwa ta intanet.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.