Hajjin Bana: Gwamnan Kano Ya Rabawa Alhazan Jiharsa Kudi Miliyan 65

Hajjin Bana: Gwamnan Kano Ya Rabawa Alhazan Jiharsa Kudi Miliyan 65

  • Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida ya gwangwaje mahajjatan jihar da tagomashin alkhairi
  • Abba ya baiwa alhazan jiharsa 6,179 zunzurutun kudi naira miliyan 65 a matsayin barka da Sallah
  • Wannan wani tanadi ne na musamman don tabbatar da ganin mahajjatan sun kasance cikin kwanciyar hankali da jin dadi yayin da suke kasa mai tsarki

Saudiyya - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da gudunmawar naira miliyan 65 domin a rabawa alhazan jihar 6,179 a matsayin barka da Sallah.

Ya ce gudunmawar na daga cikin tagomashin da jihar ta yi domin tabbatar da ganin cewa alhazan sun samu kwanciyar hankali da jin dadi yayin da suke aikin hajji, Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan Kano, Abba Gida Gida tare da Maniyyata
Hajjin Bana: Gwamnan Kano Ya Rabawa Alhazan Jiharsa Kudi Miliyan N65 Hoto: @EngrAbbaKYusif
Asali: Facebook

Cikin kujeru fiye da 95,000 da aka baiwa hukumar aikin hajji ta Najeriya (NAHCON) a 2023, Kano ce ta biyu a cikin jihohin da ke da alhazai mafi yawa inda mahajatta 6,179 suka samu tafiya hajjin bana a jihar.

Kara karanta wannan

Ana Wata Ga Wata: An Kama Kwamishinan Ganduje Kan Badakalar Biliyan 1

Dalilin rabawa mahajjatan kudi

Da yake jawabi ga manema labarai yayin wata ganawa da jami'an kananan hukumomi 44 a garin Makkah, babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta Kano, Alhaji Lamin Rabiu Danbappa, ya ce gwamnan ya ga ya zama wajibi a ci gaba da tallafawa ayyukan ibadar maniyyatan a kasar Saudiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabiu Danbappa bayyana cewa an baiwa kowani mahajjaci kudin Saudiyya riyal 50.

Babban daraktan ya kuma bayyana cewa an bayar da tallafin ne saboda kyawawan halayyar da mahajjatan suka nuna a kasa mai tsarki, rahoton Leadership.

Ya bukaci mahajjatan da su kashe barka da sallan da gwamnan ya basu da guzirinsu yadda ya dace, sannan su guji siyayya mara amfani don yana iya kawo tangarda ga shirin komawarsu gida bayan aikin hajjin.

Ya kuma bukaci mahajjatan da su ci gaba da fito da martabar jihar d kasar a kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir Ya Bayyana Watan Da Za A Fara Tallafin Karatu Na Dalibai Zuwa Kasashen Waje

An kama tsohon kwamishinan Abdullahi Ganduje kan badakalar biliyan N1

A wani labarin kuma, Legit.ng ta kawo a baya cewa hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta kwamushe tsohon kwamishinan ayyuka na zamanin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kan badakalar kudi naira biliyan daya.

An zargi Idris Wada Saleh da wasu mutane biyar da wawure kudin da sunan na gyaran tituna 30 da magudanar ruwa a cikin birnin. Sai dai kuma bincike ya nuna ko yabe ba a yi ba a hanyar kuma ba a bi ka'ida wajen cire kudaden ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng