Bankin Duniya Ya ba Ministar Shugaba Buhari Aiki Daga Barin Gwamnatin Najeriya
- Zainab Shamsuna Ahmed za ta zama babbar Darekta mai iko a bankin Duniya da ke kasar Amurka
- Tsohuwar Ministar za tayi aiki tare da tsohuwar Ministar kasar Afrika ta Kudu, Ayanda Dlondlo
- Kafin samun wannan matsayi, Zainab Ahmed ta yi shekaru fiye da bakwai ta na kan kujerar Minista
Abuja – Tsohuwar Ministar tarayya, Zainab Shamsuna Ahmed ta samu aiki da bankin Duniya a matsayin babbar Darekta mai iko.
Vanguard ta kawo rahoto a farkon makon nan cewa Zainab Shamsuna Ahmed za ta zama Darekta, kwanaki bayan ta bar kujerar Minista.
Idan abubuwa sun tafi yadda ya kamata, tsohuwar Ministar za ta fara aiki a bankin Duniya da ke kasar Amurka a ranar 10 ga watan Yuli.
An samu abin magana
Sai dai samun wannan kujera da Zainab Ahmed ta yi ba zai zo ba tare da korafi ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rahoton ya nuna cewa ana zargin masaniyar tattalin arzikin ta saba doka domin ta mika kan ta a lokacin da aka bukaci ta bada sunan wani.
Zargin da ake yi shi ne bankin Duniyan ya bukaci sunayen masana tattalin arziki uku daga wajen Muhammadu Buhari a lokacin ya na ofis.
Ana tuhumar Ahmed da cewa a lokacin ta na Ministar kudi, tattalin arziki da tsare-tsaren kasafi, ta ki ba bankin sunan kowa, ta boye maganar.
Jaridar ta ce sabuwar Darektar ba ta nemi amincewar Buhari ba, haka zalika magajinsa, Bola Ahmed Tinubu bai da masaniya kan batun.
Ba yau aka fara ba
Wata majiya ta ce an yi haka a lokacin Dr. Goodluck Jonathan ya na mulki, kuma an bada sunan Darekta Janar na ofishin kasafin kudi ne.
'Yar Najeriyar za tayi aiki a karkashin Ayanda Dlondlo wandaita ce babbar Darektan.
Bisa al’ada, Ministocin tattalin arziki da manyan Sakatarorin gwamnatin tarayya su ka saba rike wannan kujera a bankin da yake Washington.
Tinubu: Za a nada Ministoci
Kamar yadda aka yi a lokacin Umaru ‘Yaradua da Goodluck Jonathan, an samu labari wasu Sanatoci masu-ci za su zama Ministocin tarayya.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai zagaye majalisar FEC da kwararrun masana tattalin arziki, amma zai dauki wasu daidaikun Sanatoci.
Asali: Legit.ng