Dangi Sun Yi Magana Kan Zargin Matar ‘Dan Takaran APC da Lalata da Yaron Tinubu

Dangi Sun Yi Magana Kan Zargin Matar ‘Dan Takaran APC da Lalata da Yaron Tinubu

  • Ana yawo da mummunar jita-jita cewa Seyi Tinubu ya na neman Dr. Elizabeth Jack Rich da lalata
  • ‘Yan uwan Attajirin ‘dan siyasar sun fitar da jawabi na musamman, su ka wanke maid akin shi
  • I.J. Ibiwari ya yi magana da yawun Jack Rich, ya na karyata batun da ya ce ya fito daga ‘yan siyasa

Abuja - Dangin Jack-Rich ya karyata munanan zargin da ake yi wa Elizabeth Jack-Rich da samun alakar banza da ‘dan shugaban kasa, Seyi Tinubu.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin dangin ‘dan takaran shugaban kasar, The Cable ta ce an wanke Elizabeth Jack-Rich daga zargin da ake yi mata.

Cif I.J. Ibiwari ya fitar da sanarwar da ta shiga hannun ‘yan jarida, inda aka ji ya na cewa wasu ne su ka yada labarin karya domin neman cin mutunci.

Kara karanta wannan

Watakila Tsofaffin Ministocin Buhari Su Dawo Cikin Ministoci da Tinubu Zai Nada

Jack-Rich
Jack Rich da matarsa, Elizabeth Jack-Rich Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

I.J. Ibiwari yake cewa abokan adawa ne su ke nufin bata sunan Misis Jack-Rich da ‘ya ‘yanta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabin da I.J. Ibiwari ya fitar

"Mutanen da ba su da kwarewar komai illa rike kujerun siyasa sun kafa gungun masu neman bata mutane a gida da waje saboda burinsu na 2027.
Wannan makurar kasancewa ido a rufe ne ga masu neman burmawa gidan da su ka yi fada da shi. Salonsu shi ne su kai hari sannan su shiga.
Yanzu su na son shiga gidan ta hanyar kai hari ga wadanda su ka gina inda su ka taba fada a kai."

- Cif I.J. Ibiwari

An wanke Dr. Elizabeth Jack Rich

Punch ta ce jawabin ya kara da cewa Dr. Elizabeth mace mai mutunci wanda ta san darajar aure, kuma wanda ta samu tarbiyar kwarai ta Yarbawa.

Kara karanta wannan

Allah Daya Gari Banban: Yadda Aka Sha Shagalin Bikin Wani Basarake Da Amaryarsa Kada

Dangin ‘dan siyasar su ka kara da cewa uwargidarsa mata ce mai basira, kyakkyawar da ta fi karfin ayi amfani da ita, sannan uwa ga ‘ya ‘yanta.

A daidai wannan lokaci da aka zargi ‘yan siyasa da neman ci mata zarafi, dangin mai gidanta sun nuna su na tare da Dr. Elizabeth Jack Rich dari bisa dari.

Biyan kudi domin samun mukami

Jack-Rich ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, amma bai iya yin nasara ba. An ji labari daga baya aka ce ya na neman zama Minista.

Ana rade-radin 'dan kasuwan ya biya N500m saboda a ba shi kujerar Minista, amma ya karyata zargin, ya ce 'yan adawa ne su ka firgita da daukakarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel