Watakila Tsofaffin Ministocin Buhari Su Dawo Cikin Ministoci da Tinubu Zai Nada
- Adebayo Shittu zai iya komawa kan kujerar da ya bari na Ministan harkokin sadarwa a FEC
- ‘Yan Elites Coalition for Good Governance sun roki a ba Ambasada Musa Mohammed Minista
- Kungiyar ta bi ta hannun Sakataren gwamnatin tarayya, ta bada sunayen wasu da ta ke so a ba kujeru
Abuja - Idan ba dai abubuwa sun canza ba, Oserheimen Osunbor da Musa Mohammed za su iya shiga cikin wadanda za a ba kujerun Ministoci.
A ranar Litinin, Vanguard ta kawo rahoto cewa Farfesa Oserheimen Osunbor da Ambasada Musa Mohammed za su iya samun wadannan mukamai.
Farfesan da kuma Jakadan Najeriyan na cikin mutane biyu da kungiyoyin siyasa su ka bada sunayensu a sakamakon aikin da su ka yi wa jam'iyyar APC.
‘Yan Elites Coalition for Good Governance sun kai sunayen wasu ga sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, su na neman alfarmarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Adebayo Shitu zai dawo FEC?
Na uku da ‘yan kungiyar su ke so ayi la’akari da shi wajen nada Ministoci shi ne Adebayo Shitu.
Legit.ng Hausa ta na da labari Shitu ya rike kujerar Ministan sadarwa a gwamnatin Muhammadu Buhari, kafin a canza shi da Dr. Isa Ali Pantami.
Rahoton ya ce inda tsohon Ministan zai samu matsala shi ne ana tunanin an ba Gwamnan Oyo, Seyi Makinde zabi ya kawo Minista daga jiharsa.
Duk da ya na jam’iyyar PDP, Gwamnan da sauran ‘Yan G5 sun taimaki Bola Tinubu a kan Wazirin Adamawa, , Alhaji Atiku Abubakar a zaben 2023.
Kungiya ta canza suna
Kungiyar nan ta Northern Elites for Good Governance ta mutanen Arewa ce ta rikida ta zama Elites Coalition for Good Governance bayan an yi zabe.
Limaman Kiristoci A Arewacin Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Kona Alkur'ani A Sweden, Sun Bayyana Mataki Na Gaba
‘Yan kungiyar siyasar su na ganin cewa irin kokarin da su ka yi wa jam’iyyar APC da Tinubu daga gida zuwa gida ya cancanci su tsaida Ministoci.
Wadannan ‘yan siyasa uku da aka bada sunayensu su na cikin ‘yan kungiyar. Abin da ba a sani ba shi ne ko Tinubu zai amince ya ba su mukaman.
Korafin Onah, Ogharama, Orunefe da Inana
An ji labari wasu jagororin APC a Delta sun zargi Ovie Omo-Agege, Peter Obi da ‘Yan Obedient da kulla yarjejeniyar goyon bayan Peter Obi a 2023.
'Yan siyasar su ka ce wannan ya jawo aka zabi Peter Obi a zaben shugaban kasa da Omo Agege a zaben Gwamna, a maimakon ayi APC sak a Delta.
Asali: Legit.ng