Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi da Rahoton EU Kan Zabukan 2023, Ta Ba da Dalilai

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi da Rahoton EU Kan Zabukan 2023, Ta Ba da Dalilai

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da rahoton karshe na tawagar sa ido kan zaben 2023 ta kungiyar Tarayyar Turai (EU), inda ta bayyana shi a matsayin aikin da bai yi kyau ba
  • Gwamnati ta soki rahoton, kana ta bayyana cewa bayanansa sun dogara ne da jita-jita, sharhin jama’a kafofin sada zumunta da babatun 'yan adawa.
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake ya ce zabukan 2023 sahihai ne, an yi su cikin lumana, kuma mafi kyawun tsari tun 1999

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Villa, Abuja Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton karshe na tawagar sanya ido kan zabukan 2023 ta kungiyar Tarayyar Turai (EU) kan abubuwan da suka gani a zaben 2023.

Dele Alake, mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Dakyar na sha: Da jini na ya hau idan na fadi zaben sanata, tsohon shugaban APC ya magantu

Gwamnatin tarayya ta bayyana rahoton na tawagar EU a matsayin aikin zaman tebur da aka yi shi a zaune, kuma mara kyau.

Gwamnatin Tinubu ta caccaki EU game da rahoton zaben 2023
Bola Tinubu a lokacin da yake karbar takardar shaidan lashe zaben 2023 | Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ta ce tawagar ta EU ta yi tattara takaitattun bayanai ne game da zaben, inda ta kara da cewa kungiyar ta dogara ne da jita-jita, sharhin a kafafen sada zumunta da kuma babatun da jam'iyyun adawa suka yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zaben 2023: 'Yan Najeriya sun gamsu da Tinubu, in ji Alake

Alake ya ci gaba da cewa rahoton kungiyar EU kan zaben ba zai wani tasiri ba, yana mai cewa kasar ta riga da ta gamsu da shugabancin Bola Ahmad Tinubu.

Daga karshe, ya bukaci kungiyoyi da kasashen waje da su kasance masu adalci wajen tafiyar yin nazari ga abubuwan da ke faruwa a Najeriya.

A cewarsa:

"Muna kira ga EU da sauran kasashe waje da su kasance masu adalci a duk nazarin da suke yi na harkokin cikin gida na kasarmu kuma su bar Najeriya ta numfasa."

Kara karanta wannan

Yadda Yan Daba Suka Caccaki Wani Dan Kasuwa Har Lahra a Jihar Kano

Idan baku manta ba, a baya kungiyar ta bayyana cewa, akwai lam’a a zabukan da aka gudanar a kasar nan a farkon 2023.

Gwamnatin Buhari ta gano kasashen Turai na daukar nauyin ta'addanci, sun sha suka

A wani labarin, gwamnatin Buhari ta zargi kasashen waje da daukar nauyin ayyukan ta’addanci da kuma ruruta wutar rigima.

Hakazalika, ta caccaki yadda wasu kasashen duniya ke ba kungiyar ta’addanci ta IPOB goyon baya a wasu lokuta mabambanta.

Minista Lai Mohammed ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci Washington DC domin tattaunawa da manyan kafafen yada labarai na kasa da kasa game da zaben 2023 da aka kammala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.