Rayuka Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Osun
- Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan mutum biyu suna cikin tafiya a jihar Osun
- Hatsarin motan wanda ya auku akan titin Ife-Ondo ya auku ne a dalilin cika gudu da tangarɗar da burkin wata mota ya samu
- An janyo hankalin direbobi da su riƙa kulawa sosai wajen yin tuƙi domin kiyaye salwantar da rayuka ba gaira ba dalili
Jihar Osun - Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Osun, ta bayyana cewa aƙalla rayukan mutane biyu ne suka salwanta a wani hatsarin mota da ya auku akan titin hanyar Ife-Ondo.
Hukumar ta yi bayanin cewa hatsarin ya auku ne a dalilin gudu ba bisa ƙa'ida ba da ɗaukewar burki, rahoton Premium Times ya tabbatar.
Kwamandan shiyya na hukumar, Henry Benamesia, shi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Agnes Ogungbemi, ya fitar ranar Lahadi a birnin Osogbo.
Hatsarin ya auku ne a dalilin cika gudu akan titin, Benamesia
Benamesia ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne a yankin Ifetedo na jihar Osun lokacin da wata mota mai ɗauke da lambar BWR 909 SD ta ƙwace saboda gudun da ake shararawa da ita akan titin, cewar rahoton Vanguard.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya bayyana cewa mutum biyu ne suka rasa rayukansu a hatsarin sannan ƴan'uwansu da ke a wajen da hatsarin ya auku sun tafi da gawarwakinsu.
A kalamansa:
"Tawagar kai ceto ta ciro wata mota da ta faɗa cikin rafi sannan aka miƙa ta a hannun ofishin ƴan sandan Ifetodo."
"Sauran hukumomin tsaro sun zo wajen domin bayar da na su taimakon da tabbatar da doka da oda."
A cewarsa masu ababen hawa yakamata su daina cika gudu wanda ka iya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
"Ina son na yi kira ga masu zirga-zirga akan tituna da suka lura sosai sannan su yi tuƙi mai tsafta domin kare rayuka." A cewarsa.
Hukumar FRSC Ta Kara Samun Karfin Iko
A wani labarin kuma, kotu ta tabbatar hurumin hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) na cin tarar masu saɓa dokokin tuƙi.
A yanzu hukumar tana da ikon kama motoci da cin tarar duk waɗanda ta cafke suna saɓawa dokokin tuƙi.
Asali: Legit.ng