Daukar Nauyin Karatu Na Shekara 1, Alawus Din N200k: Gwamnatin Edo Ta Gwangwaje Aminat Yusuf
- Gwamnatin jihar Edo ta sanar da cewar za ta ba dalibar da kafa tarihin da ba'a taba ba a jami'ar Lagas, Yusuf Aminat, albashin lauyan jiha
- Gwamna Godwin Obaseki ya ce Yusuf za ta dunga karbar alawus din N200,000 duk wata sannan za a dauki nauyin karatunta na makarantar lauyoyi
- Obaseki ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da karrama yan asalin Edo masu hazaka a duk inda suke a duniya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Benin City, jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sanar da cewar gwamnatinsa ta karrama Aminat Yusuf da aiki kai tsaye.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni, Obaski ya ce za a dunga biyan Yusuf alawus da ya yi daidai da albashin lauyan jiha, wanda ya kai N200,000.
Aminat Yusuf: Za mu ci gaba da karrama hazikanci", Gwamnan Edo ya sha alwashi
Gwamnatin jihar ta kudu maso kudu ta kuma yi alkawarin karrama yan asalin jihar da suka nuna hazikanci a duk inda suke, jaridar The Guardian ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Obaseki ya rubuta:
"Za mu karrama hazikar daiyarmu, Yusuf Aminat da aiki kai tsaye a cikin gwamnati sannan za mu dauki nauyin karatunta a makarantar lauyoyin Najeriya na shekara daya, inda za ta dunga karbar alawus da ya yi daidai da albashin lauyan jiha, wanda ya kai kimanin N200,000.
"A matsayinmu na gwamnati, za mu ci gaba da karrama hazikanci da karrama 'ya'yanmu maza da mata da suka kawo abun alfahari ga jihar."
Bugu da kari, Obaseki ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta dauki nauyin Yusuf zuwa makarantar lauyoyi.
Aminat Yusuf: Gwamnan Legas Ya Bai Wa Dalibar Da Ta Karya Tarihin Shekara 40 Na LASU Kyautar Miliyan 10
A baya mun ji cewa, gwamnan Jihar Lagas, Babajide Olusola Sanwo-Olu , ya bai wa Aminat Yusuf, dalibar bangaren shari'a a jami'ar jihar Legas (LASU), naira miliyan 10 saboda samun sakamako mafi kyawu, wato CGPA na 5.0.
Sanwo-Olu ya sanar da bai wa Aminat gudunmawar naira miliyan 5 a karan kansa, da kuma wata naira miliyan 5 daga gwamnatin jihar.
Asali: Legit.ng