Kano: Abba Gida Gida Ya Fadi Lokacin Da Tallafin Karatu Na Dalibai Zuwa Kasashen Waje Zai Fara Aiki
- Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana lokacin da rukunin farko na dalibai masu tafiya kasashen waje za su fara karatu
- Gwamnan ya ce sun shirya tsaf don ganin rukunin farko na daliban sun fara karatu a jami'o'i daban-daban zuwa watan Satumba
- Gwamna Abba Kabir shi ya bayyana haka yayin ziyarar da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kai masa na murnar bikin sallah
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa rukunin farko na tallafin karatun kasashen waje zai fara ne a watan Satumba.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren rikon kwarya na yada labaran gwamnan, Hisham Habib a ranar Asabar 1 ga watan Yuli a Kano.
Abba Gida Gida ya bayyana haka yayin ziyarar da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kawo masa a ranar sallah.
Abba ya ce za su inganta harkar ilimi a Kano don dalibai su samo abin dogaro
Gwamnan ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da inganta harkokin ilimi a jihar, Daily Trust ta tattaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kara da cewa shirye-shirye sun kankama don sake bude manyan makarantu guda 20 da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta rufe.
Gwamnan ya godewa Sarkin, inda yabawa sarakunan gargajiya kan gudumawar da suke bayarwa a fannin kawo zaman lafiya.
Sarki Bayero ya roki gwamnan akan samar da takin zamani a Kano
Tun farko a jawabinsa, Sarki Bayero ya roki gwamnan ya samar da takin zamani ga manoma a farashi mai rahusa, cewar Daily Nigerian.
Ya kuma bukaci da a ci gaba da shuka bishiyoyi don rage zaizayar kasa tare da samar da ruwan sha a jihar.
Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Makudan Kudade, Ya Daukar Musu Muhimman Alkawura 3
Ya kirayi gwamnatin da ta yi duk mai yiyuwa don inganta tattalin arziki don masu zuba hannun jari wanda zai kawo ci gaba a jihar Kano.
Mun Kashe Biliyan 20 Kan Tallafin Karatu, Ganduje Ya Mayar Wa Abba Kabir Martani
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsu ta kashe makudan kudade kan tallafin karatu.
Ganduje ya ce akalla sun kashe fiye da N20bn a lokacin mulkinsu don inganta ilimi a jihar.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin mayar da martani ga gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Legit.ng