Karya Ne, RMAFC Ba Ta Amince da Karin Albashi Ga Tinubu, Shettima, Da Sauran Jiga-Jigan Gwamnati Ba

Karya Ne, RMAFC Ba Ta Amince da Karin Albashi Ga Tinubu, Shettima, Da Sauran Jiga-Jigan Gwamnati Ba

  • Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta hannun hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta RMAFC ta amince da karin albashin kashi 114% ga dukkan zababbun 'yan siyasa.
  • Kwanan nan, RMAFC ta kammala shirye-shiryen fara aikin bitar albashin masu rike da mukaman siyasa da na gwamnati a kasar nan
  • Duk da cewa hukumar ta ba da shawarar karin albashin ba kafin zuwan gwamnatin Bola Tinubu a watan Mayu, amma har yanzu ba ta amince da batun karin ba

Wani labarin da ake yadawa na karin 114% ga albashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da zababbun masu rike da mukaman siyasa na tarayya da na jaha da kuma jami’an shari’a, ya jawo cece-kuce a watan Yuni.

Daily Trust ta ruwaito a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, cewa gwamnatin tarayya tare da taimakon hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta RMAFC sun amince da karin albashi da 114% ga daukacin zababbun masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Daba Suka Caccaki Wani Dan Kasuwa Har Lahra a Jihar Kano

Bola Tinubu ba zai samu karin albashi ba, inji binciken gaskiya
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu | Hoto: @OfficialBAT
Asali: Twitter

Rahoton karin albashi ga Shugaba Bola Tinubu, Kashim Shettima, da sauransa akwai kuskure

A kan haka ne, Dubawa, wani dandalin yanar gizo na tantance gaskiyar labarai ya gudanar da bincike.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da yake gaskiya ne cewa hukumar ta ba da shawarar karin 114%, amma shawarar sai ta samu amincewa daga bangaren zartarwa da ma majalisa - wanda har yanzu ba a yi shi ba.

Christian Nwachukwu, jami’in hulda da jama’a na RMAFC, ya kuma fayyace cewa har yanzu shugaba Tinubu bai amince da batun ba, kamar yadda Dubawa ya bayyana.

Don haka rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ba daidai ba ne kuma akwai lam'a a cikinsa da dole 'yan Najeriya su kula don kaucewa riko da labarin da ba na gaskiya ba.

Kara karanta wannan

FG Na Fuskantar Matsin Lamba Yayin da Aka Nemi Ta Dokubo Kan Barazanar Da Ya Yi Wa Inyamurai

Tinubu ya gana da Shugaban kasar Guinea Bissau

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya gana da Shugaban kasar Guinea Bissau yayin da ya kawo masa ziyara a jihar Legas.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Tinubu ke ci gaba da hutun babbar Sallah bayan dawowarsa daga birnin Landan.

Ya zuwa yanzu, ba a bayyana abin da Shugabannin biyu suka tattauna a kai ba, amma ana kyautata zaton alaka ce mai kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.